Jam’iyyar NNPP ta yi watsi da hukuncin kotun sauraren zaben gwamnan Kano, ta ce wannan abin dariya ne a ce an tsige dan takararta, gwamna Abba Yusuf, wanda nasararsa ta fito fili.
A cikin wata sanarwa da shugaban Jam’iyyar na kasa, Kawu Ali, ya fitar, ya ce NNPP ta samu bata yarda da yadda kotun ta yanke hukuncin a shari’ar zaben gwamnan Kano ba, inda ta kira hukuncin da rashin adalci.
Jam’iyyar NNPP ta ce, za ta daukaka kara kan hukuncin kotun, kazalika shugaban ya yi kira ga mambobin kungiyar da magoya bayansu da su kwantar da hankalinsu yana mai cewa hukuncin ba zai tsaya anan ba.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da Odita na kasa kuma mukaddashin sakataren yada labarai na kasa, Oladipo Johnson, ya ce jam’iyyar har yanzu ba ta karanta hukuncin ba kuma kotu ba ta da dalilin tsige gwamnan nasu.
A wani labarin na daban hukumar ‘yan sandan Jihar Kano ta gargadi mazauna Kano cewa za a kama wadanda suka karya doka, za kuma su fuskanci fushin hukumar.
Kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba rundunar ‘yan sandan Nijeriya tare da jami’an tsaro na cikin gida damar tabbatar da doka da oda a fadin jiha.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ta bukaci Jama’ar jihar da su bayar da goyon bayasu Kamar yadda ake bukata.
Rundunar ta ce tuni aka aike da Jami’an tsaro hadin gwiwa zuwa lungu da sako a fadin Jihar don tabbatar da aiwatar da dokar ta-baci na Sa’o’i 24 don tabbatar da bin doka kamar yadda gwamnatin jihar ta sanar a wasika mai lamba: K/SEC/H/435/T.1/153 mai kwanan wata 20 ga Satumba, 2023 wanda zai fara aiki daga karfe 6 na yammacin Laraba, 20 ga Satumba zuwa karfe 6 na yammacin Alhamis, 21 ga Satumba, 2023.
Source: LEADERSHIPHAUSA