Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano ta musanta rade-radin da ake na cewa akwai wata yarjejeniya a kasa da dan takarar gwamnanta na jihar, Abba Kabir Yusuf ya yi na yafe wa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara idan ya ci zabe.
Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da lauyan dan takarar Barista Abba Hikima, ya fitar a ranar Litinin.
“Muna son jan hankalin mutane kan wani bidiyo da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewar akwai yarjejeniya tsakanin dan takarar gwamnanmu Abba Kabir Yusuf da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara na ganin an sake shi idan muka ci mulki.
“Dan takararmu ya nesanta kansa da wadannan kalamai inda ya ce babu wata hujja da za ta nuna ya yi wannan alkawari.”
Tun da fari sai an yada wani bidiyo inda ake ikirarin Abba Kabir Yusuf na shirin sakin Abduljabar da zarar ya lashe zaben gwamnan Kano da za a yi a ranar 11 ga watan Maris.
Labarin ya karade kafafen sada zumunta ne bayan da dalibin Abduljabbar, Nasir Almaliky Kabara ya wallafa sakon.
Amma a cikin wani bidiyo da ya sake wallafawa ya bayar da hakuri tare da janye kalamansa da ya yi.
A halin da ake ciki yanzu dai jam’iyyar NNPP ta samu gagarumar nasara a zaben da aka gudanar na shugaban kasa, Sanatoci da na ‘yan majalisar tarayya.
Jam’iyyar ta kashe kananan hukumomi 36 yayin da jam’iyyar APC mai mulki a jihar ta lashe kananan hukumomi takwas.
A wani labarin na daban rudani ya biyo bayan lashe zaben Sanata da Rufai Hanga na jam’iyyar NNPP da ya yi a ranar Asabar.
Amma tun kafin shiga zaben, Sanata Shekarau ya bayyana cewar tuni ya fice daga jam’iyyar NNPP kuma ba shi da wata alaka da jam’iyyar.
Kuma ya ce ya aike wa da INEC a rubuce cewar ya fice daga jam’iyyar amma ta sanar da shi cewar lokacin sauya sunan dan takara ya wuce.
Ita ma a nata bangaren, jam’iyyar NNPP ta ce ta sanar da INEC sauya sunan Shekarau da na Rufai Hanga biyo bayan ficewarsa daga jam’iyyar tare da komawa PDP.
Sai dai INEC ba ta aminta da wancan sauyi da jam’iyyar ta yi ba.
Amma ana tunanin NNPP na iya garzayawa kotun kararrakin zabe don kalubalantar ayyana Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaben.