Jam’iyyar NNPP ta kai korafinta ga hukumar kula da harkokin shari’a ta Nijeriya (NJC) kan kalaman rashin dacewa da mai shari’a Benson Anya ya yi kan jam’iyyar da mambobinta a lokacin kotun ta Kano ke yanke hukunci kan karar zaben gwamnan Kano.
Mai shari’a Anya ya yi zargin cewa, “A maimakon a bar wasu ‘yan siyasar a Kano su yi amfani da ‘yan fashin Siyasa da tashe-tashen hankula wajen kawar da dimokuradiyya a Jihar Kano, za a yi amfani da adalci wajen hana su ruguza dimokaradiyya a Kano zuwa sama.”
Jam’iyyar NNPP ta sha kaye a kotun sauraron kararrakin zaben gwamna a karar da jam’iyyar APC ta shigar.
Da yake zantawa da manema labarai a Kano, shugaban jam’iyyar na jihar, Hashimu Dungurawa, ya ce a bayyane yake cewa ba a yi wa jam’iyyar adalci ba.
A cewarsa, jam’iyyar ta kai korafinta NJC akan kalaman alkalin.
“Hakika, wadannan kalamai na batanci, da kuma la’antar da aka yi mana, musamman ma kalaman mai shari’a Benson Anya ya wuce ka’idoji da tanadin shari’a” in ji shi.
A wani labarin na daban kungiyar Kwadago a Nijeriya NLC da takwararta ta TUC, a ranar Talata za su tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani, don nuna rashin amincewa da gazawar gwamnatin tarayya wajen aiwatar da matakan masu kyau bayan cire tallafin man fetur.
Yajin aikin da ake sa ran zai fara da tsakar daren ranar Talata 3,ga watan Oktoba, 2023.
Da Yuyuwar yajin aikin zai gurgunta duk wasu harkokin tattalin arziki a fadin kasar sakamakon umarnin na kungiyar Kwadago na ma’aikata su kauracewa wajen ayyukansu.
A wani taron hadin guiwa da ‘yan kungiyar ta NLC da TUC suka gabatar na gaggawa da majalisar zartarwa ta kasa (NEC), sun zargi gwamnatin tarayya da gazawa wajen samar da ci gaba mai ma’ana kan batutuwan da suka dabaibaye Nijeriya bayan cire tallafin Fetur.
Kungiyoyin sun bayyana gwamnatin tarayya da rashin tabuka komai kan magance matsalolin da kungiyar kwadagon suka gabatar mata da su.
Source: LEADERSHIPHAUSA