Jam’iyyar NNPP ta gargadi mambobinta da ‘yan takararta kan kulla yarjejeniyar hada kai da kowace jam’iyyar siyasa domin lashe zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokoki da za a yi.
Jam’iyyar ta yi wannan gargadin ne a wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Mista Agbo Major, ya fitar a ranar Lahadi a Abuja.
Major ya shawarci ‘ya’yan jam’iyyar da su mai da hankali, su kuma zage damtse wajen yakin neman zabe tare da tabbatar da cewa sun kammala zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da za a gudanar a ranar 11 ga watan Maris a fadin kasar nan.
Major ya ce hukumar zabe ta kasa (INEC) ta yi wa NNPP rajista a shekarar 2002 kuma jam’iyyar tana kara samun nasara da fadada iyakokinta a fagen siyasar kasar a kowace da’irar zabe.
A wani labarin na daban Barista Umar Mustapha (Otumba Ekiti), dan takarar kujerar gwamna karkashin jam’iyyar LP a jihar Adamawa, ya janye daga takara, ya kuma goyi bayan takarar ‘yar takarar kujerar gwamna a jam’iyyar APC, Sanata Aishatu Dahiru Binani.
Otumba ya bayyana haka ne a taron manema labarai a ranar Asabar a Yola, wanda ya ce, ya janye daga takara, haka kuma da dukkanin tsare-tsaren yakin neman zabensa sun marawa Sanata Aishatu Dahiru Ahmad Binani, ‘yar takarar gwamnan jam’iyyar APC.
Ya ci gaba da cewa “goyon bayan takarar Aishatu Dahiru Binani ya zama tilas duba da yanayin tafiyar siyasar, kuma tana da duk abinda ake bukata a wajen gwamna, saboda haka ita ta dace da zama gwamna a jihar Adamawa” inji Otumba.