Kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar NNPP ya yi kira ga majalisar shari’a ta kasa da ta fara gudanar da bincike kan hukuncin kotun daukaka kara da ta tsige Gwamna Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar Kano.
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, Sakataren NNPP na kasa, Dipo Olayoku, ya yi karin haske game da kasancewar Engr. Abba Kabir Yusuf a matsayin cikakken Dan Jam’iyyar kuma dan Takarar Gwamnan Kano a karkashinta a ranar 18 ga Maris, 2023.
Ya ce: “A bayyane yake a gare mu cewa, abin da kawai za a iya fahimta daga wannan hukuncin shari’ar, shi ne, Kotun daukaka kara ta sauya hukuncin nasarar Gwamna Abba bayan sun kammala tattaunawa kan lamarin, sannan suka manta da cire asalin hukuncin gaskiya yayin da suke wa takardun shari’ar kwaskwarima.
“Engr. Abba Kabir Yusuf cikakken dan babbar jam’iyyarmu ne ta NNPP.
“Ya yi rajista a Unguwar Diso-Chiranchi da ke Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano. Ya bi dukkan tsare-tsare da matakai. An tantance shi a watan Mayun 2022, wanda ya kai ga zaben Firamare a watan Yunin 2022, inda ya fito a matsayin dan takarar NNPP.
“Tsarin ya samu halartar jami’an INEC da hukumomin tsaro.
Kuma INEC ta ce ta wallafa bayanan Abba Kabir dalla-dalla a Rumbun tattara bayananta.”

Source: LEADERSHIPHAUSA