Kungiyar shugabannin jam’iyyar NNPP na jihohi sun maka kwamitin gudanarwa na jam’iyyar a kotu kan rusa majalisar zartarwar jam’iyyar ba bisa ka’ida ba a jihohi 10 na tarayya.
Haka kuma Shugabannin sun zargi tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Injiniya Rabi’u Musa Kwakwaso na yin zagon kasa wanda hakan ya kawo wa jam’iyyar cikas wajen samun nasara a zaben shugaban kasa na 2023.
Sun kuma yi ikirarin cewa Kwakwaso na yin yunkurin lalata tsarin jam’iyyar, inda suka yi zargin cewa yana amfani da ‘ya’yan jam’iyyar wajen aikata laifuka da kuma daukar matakin da bai dace ba.
Da zantawa da manema labarai a Ado Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, mai magana da yawun kungiyar shugabannin na kasa, Mista Dada Olayinka Olabode ya ce rusa shugabannin jihar da kananan hukumomi na jam’iyyar a jihohi 10 ya saba wa dokar jam’iyyar.
Dada wanda shi ne shugaban NNPP na Jihar Ekiti, ya kara da cewa shugabannin jam’iyyar da ‘ya’yan jam’iyyar na damar kalubalantar Kwakwaso a lokacin da suka fahimci yadda ake gudanar da abubuwa ba daidai ba, inda suka gayyace kwamitin ladabtarwa na uwar jam’iyyar.
“Mun dauki matakin shari’a ne domin magance wannan rashin adalcin da aka yi wa mambobi sama da 7000 da suka shiga jam’iyyar a mazabu da kananan hukumomi da jihohi a Jihar Ekiti da kuma zababbun shugabannin jam’iyyar kusan 100,000 a fadin jihohi goma da wasu jihohi biyu da aka bayyana fitar da sanarwar korarsu.
“Kotun da ke Ado Ekiti ta bukaci wakilan uwar jam’iyyar su bayyana a gabanta a ranar 19 ga Satumba, 2023. Shari’ar tana gaban Mai Shari’a Aladejana na babban kotu ta 3 a da ke Jihar Ekiti”.
Kungiyar shugabannin jam’iyyar NNPP ta jihohi ta shawarci ‘yan Nijeriya, musamman ‘yan siyasa da su yi hattara da wadanda suke da alaka da jam’iyyar.
“Idan wani dan siyasa yana da sha’awar daidaitawa da jam’iyyarmu, akidarmu, falsafarmu, ya kamata ya gana da Cif Anibulam wanda shi ne uba kuma shugaban BoT na jam’iyyarmu”.
Source: LEADERSHIPHAUSA