Kungiyar yan arewa NLDM ta yi kira ga tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso ya janye daga takara.
A ‘yan makonnin nan jam’iyyar NNPP mai kayan marmari ta rasa miliyoyin mambobinta a arewa maso gabas.
Wasu kusoshin NNPP sun roki Kwankwaso ya duba abinda mutane suka fi so, ya koma bayan Atiku.
Wata kungiya da ake kira Northern Liberal Democratic Movement (NLDM) ta yi kira ga ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya janye daga tseren gaje Buhari.
Ƙungiyar ta bukaci Kwankwaso ya janye ya barwa Atiku Abubakar, mai neman kujera lamba ɗaya a Najeriya karkashin inuwar PDP, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
A cewar ƙungiyar, ra’ayin masu ruwa da tsakin arewa ya fi karkata ga Atiku, wanda ake hasshen ya fi tsohon gwamnan Kano damar lashe babban zaɓe mai zuwa.
Wannan kiran na kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren NLDM na ƙasa, Balarabe Ali Bello, ya fitar ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja.
A sanarwan, Bello ya yi ikirarin cewa ra’ayin da yan arewa suka fi karkata tsakanin mutanen biyu ya fito fili bayan jiga-jigai da shugabannin NNPP sun sauya sheka zuwa PDP.
Yace wannan ci gaban wata babbar alama ce dake nuna Atiku ka iya samun nasara a zaben watan Fabrairu.
Yadda PDP ta samu gaggarumin goyon baya a arewa Legit.ng Hausa ta tattaro cewa a ‘yan makonnin nan, jam’iyyar NNPP ta Kwankwaso ta rasa manyan jiga-jiganta, na baya-baya su ne yan takarar mataimakin gwamna a Neja da Yobe.
Shuagaban NNPP a Kaduna, Sakataren jam’iyya na shiryyar arewa maso gabas, dukkansu sun sauya sheka tare da dubun dubatar magoya bayansu zuwa PDP.
Gabanin haka, akalla mambobin NNPP 700,000 suka koma PDP a jihar Bauchi, hakan ya sa da yawan masu ruwa da tsaki suka roki Kwankwaso ya hakura ya barwa Atiku.
Ka janye ka barma Atiku – NLDM Ledership ta ruwaito Sakataren NLDM na cewa: “Ina mai shiga cikin jerin masu ruwa ɗa tsakin arewa wajen rokon mai girma Kwankwaso ya duba muradin mutanen mu ya kyale wazirin Adamawa ya ci zabe mai zuwa.”
“Bisa la’akari da yadda mambobin jam’iyyarsa ke guduwa zuwa PDP alama ce gare shi ya yi abinda ya dace game da bukatar yan arewa da ƙasa baki ɗaya.”
A wani labarin kuma Kwanaki 35 Gabanin Zabe, Babbar Kotu Ta Kori Ɗan Takarar PDP Daga Shiga Zaben 2023 Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja, ranar Jumu’an nan da ta gabata ta kara jefa jam’iyyar PDP cikin matsala ana gab da babban zabe ranar 25 ga watan Fabrairu.
Kotun ta jika wa jam’iyyar adawa aiki, inda ta kori ɗan takarar majalisar tarra kana ta umarci PDP ta shirya sabon zaben fidda gwani.
Source: LegitHausa