A ranar Litinin ne Jamhuriyar Nijar ta sake bude sararin samaniyarta bayan wata daya da sojin kasar sun kifar da gwamnatin Mohammed Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin 2023 suka kulle.
Jami’ian kasar ne suka bayyana wa kafar yada labarai ta ANP sabon matakin na bude sararin samaniyar kasar.
Mahukuntan sojin kasar sun daukin kulle sararin samaniyar ne biyo bayan barazanar daukar matakin soji da kungiyar ECOWAS ta yi sabida yin juyin mulkin.
Mai magana da yawun ma’aikatar sufuri ta kasar ya bayyana cewa, kasar ta bude daukacin sararin samaniyarta don ci gaba da zirga-zirgar Jiragen sama.
Sai dai, ma’aikatar ta bayyana cewa, ta haramtawa daukacin Jiragen soji bin sararin samaniyar ta har sai da izinin mahukuntan sojin kasar ta Nijar.
A wani labarin na daban Gwamnatin tarayya a ranar Litinin ta bukaci kungiyar kwadago ta kasa (NLC) da ta dakatar da shirinta na shiga yajin aikin gama gari na kwanaki biyu a matsayin
Source: LEADERSHIPHAUSA