Nigeria ta kulla babbar alaka da kasar Qatar
Sarkin Qatar: Sheikh Tamim Bin Hamad Al Thani, yace Qatar abude take ga yunkurin saka hannun jari na shugaba Tinubu.
A yau a birnin Doha Shugaba Bola Ahmad Tinubu da Sarkin Qatar Sheikh Tamim Bin Hamad Al Thani, suka saka hannu a wata yarjejeniya me dimbin Tarihi akan kase biyun.
Yarjejeniyar tanada niyyar bude wata kofa don yin amfani da damar hadin gyuwar juna, a fannoni dama.
Fannonin sun hada da, fannin Ilimi, habbaka masana’antu, habbaka zuba jari, karfafa matasa, ma’adinai, yawon shakatawa da sauransu.
Duba nan:👇👇
Yadda aka sa hannu a fadar shugaban kasar Qatar.
Kafin saka hannu akan yarjejeniyar da akai shugaba tinubu ya jaddadawa ma’aikata masu tarfarbaki cewa: nigeria tana maraba da masu zuba hannun jari a kasar yakuma yi nuni da tsare tsaren da ake gudanarwa, wanda ze temaka wajen samar da kirkire-kirkire, ze dawo da zuba jari da kuma al’adu daban daban.
“Babban karfin mu shine mutanen mu. Karfin mu yana cikin karfin matasan Nigeria.
Matasan suna da kuzari, da hazaka da dogaro da kai. Abokan hulda ne masu inganci ga masana’antar ta Qatar.
Suna da Ilimi da abin dogaro, kuma suna neman kara kima a duk inda suke. Wasu kadan baza su iya bawa mutane da yawa mummunan suna ba.
Matasan Nigeria a shirye suke a sako su domin amfanin kasashen biyu.
A duniya ba inda zaka sa jarinka yayi ma amfani kamar Nigeria, kasuwar da take da sama da mutum 200 yan Nigeria, masu kwazo kuma a shirye suke da suyi aiki.
“Muna fuskantar tashin hankali na gajeren lokaci a halin yanzu, amma muna da gwamnati a yau da ke nuna kwazo da hazaka na al’ummar Najeriya.
Muna aiwatar da hanyoyin da suka dace.
Wannan ƙungiyar tana aiki tare da juna da abokan aikinmu.
Najeriya a shirye take don gudanar da kasuwanci na gaske,” in ji shugaban.”
Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, ya jaddada cewa Qatar a bude take ga shugaban kasa Tinubu na sa hannun jari, inda ya tuna cewa ya yi tattaki zuwa Najeriya a shekarar 2019 saboda imanin da ya yi cewa Najeriya muhimmiyar kawa ce a karan kanta.
“Ba ni da shakku game da irin babban karfin da al’ummar Najeriya ke da shi.
A ko’ina a duniya, an san su da hazaka da aiki tuƙuru.
Sai dai mu tabbatar da cewa hakan na faruwa ne a cikin Nijeriya ba a waje ba. Zuba jarin da muka yi a duniya ya yi matukar amfani.
Wannan ya faru ne saboda muna ɗaukar lokacinmu da damar yin karatu kafin mu saka hannun jarin dukiyar jama’armu.
Ba kudina ba ne. Kudaden da muke zubawa na al’ummar Qatar ne na gaba.
Shugaba tinubu ya nada Ministan Tattalin Arziki:
Daga nan ne kuma shugaba Tinubu ya nada Ministan Tattalin Arziki da kuma Ministan Kudi, Mista Wale Edun, a matsayin jagoran tawagar gwamnatin da za ta tattauna da hukumomin Qatar wajen tantance zuba jari da aiwatar da su.
A yayin tattaunawar da aka yi tsakanin bangarorin biyu, shugaba Tinubu ya ba da damar gabatar da takaitaccen bayani ga Sarkin ta hannun Ministan Ma’adanai na Kasa, Dokta Dele Alake, wanda ya yi bayani dalla-dalla game da manyan ma’adanai da dama da suka hada da lithium, nan da nan da ake samu a fadin kasar nan tare da samar da sinadarin lithium.
Duba nan:👇👇
Ganawar sirri tsakanin shugabannin biyu
Shugabannin biyu sunyi ganawar sirri kafin a cigaba da taron sanya hannu kan yarjejeniyoyin kase biyun a bangarori da dama.