Sunny Sylvester Moniedafe, mataimakin shugaban kungiyoyin tallafi na kwamitin kamfen din dan takarar shugaban kasa na APC, Arewa maso gabas ya ce nasarar jam’iyyar na cikin hadari.
Cif Moniedafe ya yi wannan gargadin ne a yayin da ya ke janyo kan hankalin mambobin jam’iyyar su hada kai su amince da shugabancin Sanata Aisha Binani.
Jigon na jam’iyyar APC ya ce kwamitin kamfen din shugaban kasa na APC da NWC da gwamnonin jam’iyyar suka nada ta don haka su yi hakuri su hada kai don yin nasara a 2023.
direkta na kungiyoyin tallafi na kwamitin kamfen din yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a Arewa maso Gabas, Cif Sunny Sylvester Moniedafe, ya ce abin da wasu muhimman masu ruwa da tsaki a jam’iyyar a jihar Adamawa ke yi na barazana ga nasarar ta a babban zaben 2023.
Moniedafe, tsohon mai neman takarar shugaban jam’iyyar APC na kasa ya bayyana hakan ne yayin da ya tattauna da Daily Trust a ranar Alhamis a Abuja.
Ya ce yan jam’iyyar da ke ganin an zalunce su suna shirin yin yakin neman zabe ba tare da amincewa da Sanata Aisha Binani a matsayin shugaban kwamitin kamfen din shugaban kasa a jihar ba.
Moniedafe: Mu yi hakuri mu hada kai don yin nasarar a zaben 2023 Moniedafe, wanda mamba ne na kwamitin yakin neman zaben Buhari/Osinbajo a 2015 da 2019, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a jihar su yi abu yadda ya dace saboda nasarar jam’iyyar a 2023.
Ya ce: “Akwai matsaloli tattare da kwamitin kamfen din shugaban kasa na Tinubu/Shettima a Jihar Adamawa.
Amma ina son kira ga dukkan mambobin jam’iyya da ke ganin an zalunce su cewa (Sanata Aisha) Binani bata nada kanta ba, kwamitin kamfen na shugaban kasa da NWC da gwamnoni suka zabe ta.
“Sun zauna sun nada ta shugaban PCC a jihar Adamawa. Sunanan Binani yana jerin wadanda aka nada.
Ina son shawartar kwamitin NWC kada su yi son kai.
Wasu mutane sun fusata saboda wasu dalilai kuma an fada min za su yi taro a Yola, amma Namdas shima ya kira taro a ranar a Genyi.
“Amma shugaban PCC a Adamawa ita ce Sanata Binani. Idan za a yi taro ya kamata ta halarta.
Sun yi ikirarin wai ba a sanar da su ba. Kada mu raba gidan mu kafin zaben 2023 kuma masu ruwa da tsaki su sani cewa za mu fadi zabe idan ba mu tashi tsaye ba.”
Ya cigaba da cewa: “Ba mu taba samun gwamna ba a Adamawa Central.
Mun yi addu’a Allah ya bamu dan takara daga Adamawa Central kuma ya amsa.
Yanzu muna cewa ba mu son Binani. Wannan hatsari ne ga nasarar mu a 2023. A zauna lafiya.”
Jam’iyyar APC, ta tsayar da ranar 15 ga watan Nuwamban 2022, don kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasarta a Jos, babban birnin jihar Plateau.
Hakan na cikin jadawalin da jam’iyyar ta fitar ne a ranar Laraba 3 ga watan Nuwamban 2023, The Punch ta rahoto.
Source:legithausang