Najeriya ta yi watsi da yarjejeniyar da kasashen duniya suka rattaba wa hannu da zummar ganin manyan kamfanoni na biyarn haraji mai gwabi-gwabi.
Matakin bullo da sabon tsarin harajin a zuwa ne bayan an yi la’akari cewa, manyan kamfanonin kasashen duniya na dada fadada ribar da suke samu ta hanyar biyan harajin da bai-ta-kara-ya karya ba.
Yanzu haka Hukumar Bunkasa Tattalin Arziki ta Kasa da Kasa OECD ta ce, wannan yarjejeniyar za ta samar da karin Dala biliyan 150 na haraji a cikin shekara guda, abin da zai kara karfafa tattalin arzikin kasashe a daidai lokacin da suke fafutukar gyagijewa daga annobar Korona.
Ana sa ran matakin cimma yarjejeniyar ya shafi hatta manyan kamfanonin Amazon da Facebook da kuma sauran kamfanonin da ke samun kimanin cinikayyar sama da biliyan 20 na Dala da Euro.
Tun a farkon watan Yulin da ya gabata, sama da kasashe 100 suka goyi bayan sabon tsarin jim kadan da fitar da shi ga duniya, duk da a wancan lokacin an samu kasashen irinsu Ireland da Hungary da Estonia da suka ki amincewa, amma daga bisani suka shiga ciki.
Kawo yanzu, Najeriya da Kenya da Pakistan da Sri Lanka ba su amince da yarjejeniyar ba.
A wani labarin na daban har yanzu bankunan nahiyar Turai ba su daina labewa a yankunan da ke da sassauci a wajen biyan haraji ba, duk da jerin badakala da suka bankado hanyoyin da manyan kamfanonin kasa da kasa ke bi wajen kauce wa biyan haraji, a cewar wani rahoton bincike.
Wannan kaso ya kasance a yadda yake tun a shekarar 2014, a lokacin da jerin bankade-bankade kamar su Lux Leaks da Panama Papers suka kwalmata dabarun da manyan kamfanoni da masu hannu da shuni ke yi wajen kauce wa biyan haraji.
Rahoton ya ce, duk da yadda wannan batu ya yi fice har ya kasance abin muhawwara a tsakanin masu sharhi da ‘yan siyasa, bankunan Turai ba su shiga taitayinsu ba a game da yin hanya-hanya a kan biyan haraji, inda suke ci gaba da kasancewa a inda za su yi coge.
Binciken, wanda wani farfesa, kuma kwararre a fannin haraji daga jami’ar Berkeley Gabriel Zucman ya jagoranta, ya yi nazari a kan bayanai da cibiyoyin kudi 36 suka wallafa a tsakanin shekarar 2014 zuwa 2020, kuma ya mayar da hankali ne a kan bankunan HSBC, Deutsche Bank, da Societe Generale.