Kamfanin man Najeriya na NNPC ya ce ya kashe naira biliyan 100 wajen farfado da matatun man kasar da basa aiki a shekarar da ta gabata.
Yan Najeriya sun dade suna korafi a kan yadda matatun basa iya aiki kamar yadda ake bukata lura da dimbin kudaden da ake kashewa a kan su.
Shugaban rukunin kamfanonin na NNPC, Mele Kyari, ya ce an rufe matatun man Najeriya ne saboda sun gaza gudanar da ayyukansu kamar yadda ya ake bukata.
Ya yi misali da matatun man Kaduna da Warri wadanda ake bukatar su tace gangunan danyen mai har dubu 170,000 a kowace rana kafin su gudanar da kashi 70 na aikin da ya kamata su yi.
A wani labarin na daban Kamfanin NNPC a Najeriya ya sanar da kulla wani kwantiragin cinikayya tsakaninsa da wasu kamfanonin mai na Duniya 4 da suka kunshi Shell da Exxon da Total da kuma Eni, yarjejeniyar da za ta kai ga zuba jarin dala biliyan 10 a kasar.
Wasu bayanai na nuna cewa tun a talatar da ta gabata, Kamfanin man Najeriyar na NNPC da kamfanonin man 4 da suka kunshi Shell da Exxon da Total da kuma Eni sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hakar man a Bonga, karkashin lasisin OML 118 da ya sahale bayar da hayar filayen hakar mai.
Najeriyar wadda yanzu haka tattalin arzikinta ke tangal tangal sakamakon rashin daidaituwar farashin mai a kasuwar Duniya sanadiyyar annobar covid-19 sabuwar yarjejeniyar hakar man a karkashin ruwa tsakaninta da kamfanonin 4 za ta karan kudin shigar da bangaren mai ke bai wa kasar zuwa dala biliyan 780 baya ga wasu dala biliyan 9 ta daban.
Shugaban kamfanin na NNPC a sakon da ya wallafa a Twitter bayan kulla yarjejeniyar ya ce matakin zai nunawa Duniya cewa kofa a bude ta keg a masu son zuba jari a kasar.
Yankin na Bonga wanda ya koma samar da ganga dubu 90 kowacce rana tun daga watan Fabarairu sabanin ganga dubu 225 da ya ke samarwa a baya, yarjejeniyar za ta bayar da damar ninka ayyukan da ya ke.