Mako guda bayan farmakin jirgin kasa a Najeriya, alkaluman hukumar tashoshin jiragen kasar sun nuna cewa zuwa yanzu mutane akalla 168 suka bace a farmakin wanda ‘yan bindiga suka kaddamar ta hanyar dasa abin fashewa da kuma bude wuta.
A cewar hukumar fasinja 362 ne ke cikin jirgin lokacin farmakin amma 186 sun tsira da lafiyarsu yayinda 176 ko dai suka mutu ko kuma suka bace ba tare da sanin inda suke ba.
Matsalar hare-haren ‘yan bindiga musamman a babbar hanyar ta Abuja zuwa Kaduna na ci gaba da tsananta inda a kowacce rana tarin fararen hula ke rasa rayukansu.
Duk da cewa gwamnatin ta Najeriya, na ikirarin daukar matakan tsaro don tabbatar da tsare rayukan jama’a amma hare-hare na kara tsananta yayinda ba kadai bangarorin adawa ba, har ma da wadanda ke cikin gwamnati ke ci gaba da caccakar salon kama ludayin jami’an tsaron kasar a yaki da matsalar.
Kafin yanzu dai anyi ta samun jita-jita tare da barazanar yiwuwar farmakar jirgin kasan wanda ke tashi daga Abuja zuwa Kaduna amma kuma ba tare da gwamnatin Najeriya ko jami’an tsaronta sun dauki matakan da suka kamata ba.
A wani labarin na daban kuma Wani bincike a Najeriya ya bayyana cewar rashin hukunci da nuna kabilanci tare da talauci ne suka zafafa ayyukan ta’addancin da suka mamaye yankunan karkarar Jihohin dake arewa maso yammacin kasar.
Kungiyar tace ya zuwa wannan lokaci, wadannan ‘Yan bindiga sun kashe akalla fararen hula 12,000, yayin da suka tilastawa sama da miliyan guda tserewa daga gidajen su domin samun mafaka.
CDD tace tashe tashen hankulan da ake samu a jihohin dake arewa maso yamma da ya fantsama zuwa Jihar Neja dake yankin arewa ta tsakiya, matsalar da ta rikide ta zama yaki yadda ‘Yan ta’adda ke kai hari akan cibiyoyin soji da jiragen kasa da kuma hari akan matafiya a manyan hanyoyin kasar.
Cibiyar tace duk da yake ana cigaba da mahawara akan bukatar ‘Yan ta’addan da kuma abinda ke basu kwarin guiwa, CDD tayi watsi da zargin cewar mayakan boko haram da ‘Yan siyasa da Fulani na tallafawa ‘Yan bindigar.
Cibiyar tace babu yadda za’a takaita abinda ya haifar da tashin hankalin zuwa matsala guda, domin kuwa dole sai an duba batutuwa da dama da suka hada da tattalin arziki da siyasa da kuma matsalolin rayuwar yau da kullum.
CDD tace rashin hukunci akan wadanda suka aikata manyan laifuffuka da cin hanci da rashawa daga bangaren shari’a tare da bangaren ‘Yan Sanda na daga cikin dalilan da suka sa wasu daukar makamai domin samarwa kansu mafita.
Cibiyar tace kungiyoyin Sakai da ake kafawa a wasu garuruwa domin kare jama’a suma sun taka rawa wajen daukar doka a hannun su, inda suke wuce makada da rawa wajen kashe Fulanin da basu ji ba, basu gani ba, musamman a Jihar Zamfara.
CDD ta kara da cewar talauci ya kuma taimaka wajen sanya wasu mutane daukar matakai domin rashin sana’ar da za suyi su samu kudade.
Cibiyar tace babu yadda za’a yi nasarar shawo kan wannan matsala sai dole an samu hadin kan shugabannin da matsalar ta shafa da kuma karfin guiwa daga bangaren gwamnati wajen duba matsalolin tsaro da zummar shawo kan su.
CDD ta yi misali da yadda aka kashe Buharin Daji, daya daga cikin manyan Yan bindigar Jihar Zamfara, wanda matakin ya haifar da rarrabuwar ‘yayan kungiyar sa da kuma ingiza matsalar maimakon shawo kan ta.
Cibiyar tace duk wani mataki da za’a dauka na dakile wannan matsala sai ya shafi sake fasalin aikin tsaro da kuma dawo da yarda tsakanin su da jama’ar dake karkara.