‘Yan bindiga sun kashe akalla mutanen 17 a wasu hare hare da suka kai kauyuka 4 a karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Najeriya, inda suka kuma yi awon gaba da dimbim dabbobi bayan sun yi ta harbi kan mai uwa da wabi.
Wata majiya ta ce tun da tsakar ranar Alhamis ne ‘yan bindigar suka fara afka wa mutane, har ma suka shiga kasuwar Rafin Gero da ke ci, suka yi awon gaba da dimbin shanu da rakuma da sauran dabbobi.
Mazuna yankin sun ce duk da cewa mutane sun ruga cikin daji don neman tsira, ‘yan bindigar sun yi ta bin su a kan babura suna harbewa.
Ya zuwa lokacin hada wannan labari, babu wani karin bayani daga rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, kuma duk kokarin samun kakainta ya ci tura.
A wani labarin na daban Dubban mutane ne suka isa Jamhuriyar Nijar bayan da suka tsere wa rikici da ake yi tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai a arewacin Mali, kamar yadda wani rahoton majalisar dinkin duniya ya bayyana a jiya Juma’a.
Ofishin kula da ayyukan jinkai na majalisar dinkin duniya ya ce sama da fararen hula 400 ne aka yi amannar sun mutu sakamakon rikicin na kungiyoyi masu dauke da makamai.
Wasu daga cikin ‘yan gudun hjirar na karbar taimako daga hukumar abinci ta duniya.