Majalisar Dinkin Duniya ta koka kan yadda adadin mutanen da ke bata da kuma barin muhallansu dalilin yake-yake ke karuwa musamman a farkon shekarar da muke ciki.
A cikin wani rahoto da Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ta ce, daga watan Janairun bana zuwa watan Yuni mutane miliyan 84 ne suka bar muhallansu sakamakon rikice-rikice, wanda kuma kusan rabinsu ba’a ma san inda suke ba a halin yanzu.
A cewar hukumar wannan adadi ya karu da miliyan biyu, idan aka kwatanta da wanda aka samu a bara.
Majalisar ta ce, babban abin fargabar ma shi ne mafi yancin wadanda suka bar muhallansu na gamuwa da matsaloli da suka shafi lafiyar jiki da ta kwakwalwarsu da kuma barazanar cin zarafin su da bautar da su da sauran matsaloli.
Majalisar ta kara da cewa mutanen kasar Syria ne suka fi yawan wadanda suka gudu daga gidajensu sanadiyar yaki sai na Falasdinu da Afghanistan da ke biye musu baya a yawa, sai mutanen Venezuela da sauran kasashen da ake fama da rashin kwanciyar hankali.