Mutane 8 sun mutu, da dama sun samu raunuka bayan da wata mota da aka dana wa abin fashewa ta yi bindiga a kusa da wata makaranta a mogadishu, babban birnin Somalia, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana
Kungiyar Al-shabaab ta dauki alhakin wannan harin na baya bayan nan a kasar da rikici ya wa dabaibayi, inda ta ce ta nemi hargitsa wasu mutane da ke karbar horon soji ne.
Jami’in tsaro, Mohamed Abdillahi ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa tun da farko cewa fashewar ta tashi ne daga wata mota inda har dalibai 11 suka samu rauni.
Shaidu sun ce wani ayarin motoci dauke da sojojin kiyaye zaman lafiya na Tarayyar Afirka da ke yaki da ‘yan ta’adda na wucewa ta hanyar a lokacin da fashewar ta auku.
sun ce fashewar ta haddasa mummunar barna ga makarantar da kuma ababen hawa da aka ajiye a kusa da ita.
Kungiyar da ake alakanta da Al-Qaeda tana yawan kai hare hare a babban birnin kasar da sauran yankunanta, inda a kwanan nan ne ma suka kai hari kan fitaccen dan jaridar Somalia suka kashe shi.
A wani labarin na daban a Somalia, mutane da dama suka jikkata biyo bayan wani harin kunar bakin wake da aka kai tsakiyar Somaliya cikin daren jiya juma’a, inda aka bayyana mutuwar mutane 16.
A cewar wani babban hafsan sojan kasar kanal Ahmed Dahir ,dan kunar bakin wake na da niyar kai hari kan wasu manyan hafsan sojan kasar dake cikin tawagar firaministan kasar.
Wani babban hafsan sojan kasar ta wayar talho ya sheidawa kamfanin dilancin labaren faransa na Afp cewa an samu karin mutane da suka rasa rayukan s u a wannan hari na jiya.