Akalla mutane 17 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 59 suka samu raunuka, sakamakon fashewar bama-bamai a Apiate, kusa da birnin Bogoso mai tazarar kilomit 300 a yammancin birnin Accra fadar gwamnatin kasar Ghana.
Mutane na ta yada bidiyon ta’asar da wutar ta yi biyo bayan fashewar da ta wakana a yankin Apiate dake da nisan kilometa 300 a gabashin babban birnin kasar Accra da misalin karfe 12 na rana.
Mutanen wannan yankin na cikin jimami da kaduwa,inda wasu rahotanni daga yankin ke tabbatar da cewa yan lokuta kafin aukuwar iftila’in,direban motar shake da bama-bamai da wani kamfanin hako ma’adinai na yankin ke amfani da su,ya kira jama’a da su kaucewa wannan wuri yan lokuta kafin fashewar wadanan bama-bamai.
A wani labarin na daban Bankin Zuba jarin kasashen Turai ya bayyana shirin tallafawa gwamnatin kasar Ghana da kudin da ya zarce euro miliyan 80 domin inganta shirin yaki da annobar korona.
Shugaba Nana Akufo-Addo ya rattaba hannu akan yarjejeniyar karbar tallafin a wani bikin da akayi a Cibiyar bakin dake Luxembourg.
Mataimakin ministan harkokin wajen Ghana Kwaku Ampratwum Sarpong ya rattaba hannu akan yarjejeniyar a madadin kasar sa, yayin da Ambroise Fayolle, mataimakin shugaban bankin zuba jarin Turai ya sanya hannu a madadin bankin, kuma anyi bikin ne a gaban shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo da shugaban bankin Werner Hoyer.
Akufo-Addo ya bayyana cewar inganta dangantaka tsakanin bankin da kasashen Afirka na da matukar muhimmanci musamman wajen zuba jari a yankin Afirka dake kudu da sahara.
Shugaban Bankin zuba jarin Werner Hoyer ya yaba da matakin da Ghana ta dauka na rage radadin annobar korona ta hanyar zuba jari a bangaren kiwon lafiya.