Ministan watsa labaran Najeriya Lai Mohammed ya ce zuwa Juma’ar da ta gabata, ministocin 9 suka sauka daga mukamansu bayan da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya umarci su yi hakan kafin ranar 16 ga wannan wata na Mayu, bayan da suka bayyana sha’awarsu ta tsayawa takara a zabuka masu zuwa.
Bayanai sun ce a ranar Juma’a shugaban Najeriyar ya gana da dukkanin ministocin da suka ajiye ayyukansu nasu a Abuja, inda ya yi musu bankwana gami da fatan alheri dangane da aniyar da suka sanya a gaba.
A baya bayan nan daga cikin ministocin Ministan kwadago da samar da ayyukan yin a Najeriya, Sanata Chris Ngige, ya sanar da janye aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a jiya Juma’a, inda ya yi alkawarin kauracewa shiga al’amuran siyasar jam’iyyarsa ta APC mai mulki.
Rahotanni sun kara da cewar tuni shi ma Ministan Shari’a Abubakar Malami, ya janye daga takarar neman kujerar Gwamnan jihar Kebbi domin maye gurbin Atiku Bagudu.
Bayan shafe watanni ana cece-kuce kan rade-radin shiga takararsa ce, Ministan shari’ar ya shiga jerin masu neman kujerar gwamnan jiharsa ta Kebbi a watan da ya gabata.
A wani labarin na daban Gwamnatin Burkina Faso, ta ce tawagar jami’an agajin da suke aikin zuke ruwan da ya mamye wani ramin hakar ma’adinin Zinc, suna dab da kaiwa ga ceton ma’aikata takwas suka makale kusan wata guda a cikin ramin, domin dauko su daga wani sako da suka shige domin samun mafaka.
Masu hakar ma’adanan da ambaliyar ruwan ta rutsa da su dai sun hada da ‘yan Burkina Faso 6, dan Tanzania daya da kuma dan Zambia daya, wadanda suka bace tun bayan da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya mamaye filin hakar ma’adanin Zinc na wani kamfanin kasar Canada da ke garin Perkoa tun a ranar 16 ga Afrilu.
Kamfanin ya ce yayin da akasarin ma’aikatan da ke karkashin kasa suka samu nasarar tsira daga ambaliyar, sauran guda takwas sun gaza fita ne kasancewar suna da nisan mita 520, kwatankwacin kafa dubu 1 da 706 daga doron kasa.
Tun a ranar larabar da ta gabata, kakakin gwamnatin Burkina Faso, Lionel Bilgo ya ce an cire ruwan da yawansa ya zarce lita miliyan 38, a kokarin da ake yi na ceto ma’aikatan da ambaliya ta rufe a ramin hakar ma’adanan da suke tsaka da aiki a cikinsa.