Ministar Tsaron Faransa Florence Parly ta fara ziyarar aiki na kwanaki biyu a Jamhuriyar Nijar, inda ake saran zata tattauna da hukumomin kasar dangane da shirin tsaron yankin Sahel.
Wannan ya sa kasar Jamus wadda ke da sojoji dubu guda a kasar dake aikin samar da zaman lafiya a karkashin Majalisar Dinkin Duniya ta fara tababa dangane da zaman sojojin ta a Mali.
Ita ma kungiyar kasashen Turai ta bayyana cewar nan da tsakiyar wannan wata ta Fabarairu zata yanke hukunci akan bukatar janye daukacin dakarun kasashen Turai dake yaki da Yan ta’adda a Mali. Jamhuriyar Nijar na da matukar tasiri wajen yakin da Faransa keyi da Yan ta’adda a Sahel, lura da cewar wasu daga cikin sojojin ta na zama ne a kasar.
A wani labarin na daban Faransa na kara azama wajen tattaunawa da kawayenta na Turai a game da dambarwar da ke tsakaninta da kasar Mali da ke fama da tashin hankali, wadda ke barazanar rikidewa zuwa rikici tsakaninta da gwamnatin sojin Bamako.
An samar da gamayyar, wadda ta tattaro dakaru na musamman daga kasashen Turai a karkashin jagorancin Faransa don bada shawarwari ga sojojin Mali, tare da taimaka musu a fagen daga.
Al’amuran da suka auku a baya bayan sun sa dakarun Takuba sun karu zuwa dari 9, amma makomar aikin na samun cikas sakamakon gutsiri tsoma tsakanin Faransa da Mali.
Rikicin da ya kunno kai tun bayan juyin mulkin Mali na watan Agusta ya zafafa, musamman tun da sojojin Mali din suka sanar da dauko sojojin haya daga Russia, matakin da Faransa ta nuna ba ta so.
Matsalar baya bayan nan ya kunno kai ne lokacin da Mali ta bukaci dakarun Denmark da suka sauka kasar don aikin rundunar Takuba su koma, bisa dalilin cewa an gayyato su ba da saninta ba.
Ministar Tsaron Faransa Florence Parly ta caccaki wannan mataki, wanda ke zuwa mako guda bayan Mali ta nemi a sake nazarta yarjejeniyar tsaro da ke tsakanin kasashen 2.