Tashar akhabr Quds ta bayar da rahoton cewa, Yair lapid ministan gwamnatin yahudawan sahyuniya ya isa kasar Morocoo a yau Laraba.
Ministan harkokin wajen gwamnatin yahudawan ya isa kasar Morocco ne tare da rakiyar ministan jin dadin jama’a na yahudawan Isra’ila, inda suka samu gagarumin tarbe daga gwamnatin Morocco.
Lapid ya bayyana wannan rana da cewa ta tarihi ce ga Isra’ila, domin kuwa wannan yana nuni da irin karbuwar da Isra’ila take samu daga gwamnatocin larabawa.
Ministan yahudawan ya gana da takwaransa na Morocco, tare da sanya hannu a kan wasu yarjeniyoyi na yin aiki tare tsakanin gwamnatin Morocco da kuma gwamnatin yahudawan Isra’ila..
Morocco dai ta sanar da amincewa da Isra’ila a hukumance sakamakon matsin lambar da ta fuskanta daga gwamnatin Trump, tare da yi mata alkawalin cewa idan ta yi hakan, Amurka za ta amice da yankin yammacin Sahara a hukuamnce da cewa mallakin kasar Morocco ne.
A wani labarin na daban shafin yada labarai na Shehab News ya bayar da rahoton cewa, Faisal Bin Farhan ministan harkokin wajen Saudiyya ya bayyana, kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila da gwamnatocin UAE, Bahrain, Sudan da kuma Morocco suka yi, zai taimaka wajen samun ci gaba a yankin.
Ya ce a lokacin da aka gudanar da zama a yankin Al’ula na Saudiyya an samu fahimtar juna a tsakanin Saudiyya da Qatar, bayan kwashe tsawon shekaru suna zaman doya da manja.
Kafin wannan lokacin dai matsayar Saudiyya ita ce ba za ta amince da kulla alaka ta zahiri da Isra’ila ba, matukar ba a kafa kasar Falastinu a akn iyakokin shekara ta 1967 ba, wanda kuma sabon furucin ministan harkokin wajen kasar ya yi hannun riga da wannan matsaya.