Gwamnnatin Tarayyar Najeriya a ta bakin minista mai lura da harkar makamashi ta ce matsaloli masu tarin yawa ne suka haddasa karancin wutar lantarki da ake fuskanta a duk fadin kasar.
To sai dai minista na makamashi na kasar Abubakar Aliyu wanda ya sanar da hakan, ya ce yanzu haka gwamnati na iya kokarinta domin shawo kan lamarin.
Minista Aliyu ya ce daga cikinsu akwai matsalar fasa bututun mai da kuma takaddamar da ake yi tsakanin kamfanonin samar da gas da kamfanonin da ke da alhakin raba wutar lantarki a cikin kasar.
Yanzu haka dai matsalar karancin wutar lantarki da kuma rashin mai sun shafi kusan kowane fanni na rayuwa a Najeriya, da suka hada da masana’antu, sufuri da sauran muhimman sassa.
Tuni dai wasu daga cikin masu kamfanoni da masana’antun suka fara nazari game da yiyuwar rage yawan abubuwan da suke sarrafawa a rana ko kuma rufewa baki daya saboda rashin wuta da kuma tsadar gas.
Yayin da a hannu daya aka fara ganin hauhawar farashin abubuwa a kasuwannin Najeriya.