Kusan kasashen duniya 200 sun cimma wata yarjejeniyar bai-daya domin yaki da matsalar sauyin yanayi bayan sun kwashe tsawon makwanni biyu suna kiki-kaka kan yarjejeniyar, inji (MDD)
Bukatun kasashe matalauta
An soki kasashen duniya mawadata a taron na COP26 da ya gudana a birnin Glasgow saboda nokewarsu wajen samar da kudade ga kasashe matalauta wadanda kuma ke fuskantar barazanar fari da tunbatsar tekuna da tashin gobara da kuma kadawar guguwa a sanadiyar sauyin yanayi.
A yayin cimma yarjejeniyar ta magance sauyin yanayi, kasashen China da India sun hakikance cewa, dole ne a sassauta a bangaren makamashi.
Wakilan kasashen duniya dai, sun shiga tattaunawa da juna a taron ne da zummar dabbaka yarejejeniyar Paris ta 2015 wadda manufar ta ita ce, takaita dumamar yanayi da maki 1.5 a ma’aunin Celcius. Sai kuma samar da kudade ga kasashen duniya masu tasowa.
Rashin gamsuwar Majalisar Dinkin Duniya (MDD)
Tuni Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) Antonio Guteress ya yi lale marhabin da yarjejeniyar da kasashen duniyar suka cimma a birnin na Glasgow, amma a cewarsa, har yanzu fa akwai sauran rina-a kaba.