Wakiliyar ta MDD, Muruli tace yana da muhimmancin matan Najeriya su shiga a dama da su a siyasa, saboda shigar su zai bada damar daukar matakan inganta rayuwar al’umma.
Jami’ar tace da farko dai Najeriya ce ke da wakilai mata mafi karanci a Yankin Afirka dake kudu da sahara da kuma duniya, saboda haka abin takaici ne ga kasar da tafi kowacce a Afirka na rashin baiwa rabin al’ummar ta wakilcin da ya dace.
Muruli tace a zamanin da ake tafiya yanzu da mata suka fi maza yawa, yana da muhimmanci a dinga raba dai dai na mukamai, inda akalla kowanne jinsi zai samu kashi 50.
Shugabar kungiyar mata ta WIPF Ebere Ifendu ta bayyana cewar mazaje sun sace tarin kudin jama’a, saboda haka suke amfani da su lokacin siyasa domin mallake mukaman da ake da su.
Ifendu tace duk da yake basu da kudi, suna da yawan da idan sun hada kan su zasu iya yin tasiri lokacin zaben.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Ifendu na bukatar matan da su kara kokari wajen shiga siyasa a dama da su, maimakon jiran mukamai.
A wani labarin na daban jagoran Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewar ya warke sarai bayan jinyar da yayi a birnin London na makwanni.
Bayan komawar sa Najeriya yammacin jiya, Tinubu wanda ya samu tarbo daga wasu daga cikin manyan ‘Yan siyasar Lagos, cikin su harda gwamna Babajide Sanwo-Olu yace ya warke sarai daga jinyar gwuiwar da yayi fama da ita.
Rashin lafiyar Tinubu ta haifar da cece kuce a fagen siyasar Najeriya, abinda ya sa wasu fitattun ‘Yan siyasar kasar suka kai masa ziyara zuwa birnin London domin duba lafiyar sa.
Daga cikin wadanda suka ziyarci tsohon gwamnan Lagos harda shugaban kasa Muhammadu Buhari da wasu gwamnonin jihohi da shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila da mataimakin sa Ahmed Wase da ‘Yan Majalisun Dattawa da na wakilai da tsoffin gwamnoni.
Magoya bayan Tinubu na bayyana aniyar sa ta tsayawa takarar zaben shugaban kasa a shekarar 2023, kuma tuni fastocin sa suka bayyana a wasu biranen Najeriya.
Sai dai rahotanni sun ce ana ci gaba da takun saka a cikin Jam’iyyar APC dangane da takarar Tinubu wanda ke kokarin maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari sakamakon yadda wasu ‘Yan arewacin Najeriya ke adawa da shirin.
Tuni Gwamnonin kudancin Najeriya 17 suka gudanar da wani taro a Lagos inda suka bukaci mayar da shugabancin kasar zuwa ‘yankin su bayan kammala wa’adin shugaba Buhari, yayin da wasu ‘yan arewa ke cewa babu wata yarjejeniyar da akayi ta karba-karba, saboda haka ‘dan takara daga kowanne sashen Najeriya na iya neman kujerar.
A wani taro da suka gudanar a Kaduna, gwamnonin arewacin Najeriya sun bayyana rashin amincewar su da matakan da takwarorin sun a kudu ke dauka na neman shugabancin.
Wannan ya sa wasu magoya bayan Tinubu a wannan mako suka kaddamar da shirin takarar sa da suka yiwa suna SWAGA mai dauke da manufofin Yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.
Ya zuwa wannan lokaci dai, Jagoran APC bai yi shelar tsayawa takarar zaben da bakin sa ba, sai dai alamu da dama na bayyana shirin.