Majalisar dinkin duniya (MDD) ta ce kasashe masu tasowa na bukatar ninki 10 na kudaden da aka ware don kare kansu daga mummunan tasirin sauyin yanayi dake ci gaba da tsananta.
Ganin yadda guguwa, ambaliya da fari suka ta’azzara sakamakon dumamar yanayi, kasashe matalauta sun yi kira ga masu kumbar susa a taron yanayi na COP26 da su mutunta alkawarin da suka yi na samar da dala biliyan 100 duk shekara don tunkarar matsalar ta dumamar yanayi.
Rahoton hukumar kare muhallin ta majalisar dinkin duniya (MDD), ya gano cewa kasashe masu tasowa kawai za su bukaci kashin abin da ya tasamma dala biliyan 300 a cikin shekara guda zuwa shekarar 2030, da biliyan 500 zuwa 2050 wajen daukar wadannan matakan.
A Wani sabon rahoto kuma da aka wallafa jiya Alhamis ya bayyana cewa, yawan fitar da iska mai gurbata muhalli zai ta’azzara a cikin wannan shekara ta 2021 zuwa matakin da aka gani gabanin bullar cutar Korona.
Rahoton wanda aka wallafa a yayin da kusan kasashen duniya 200 ke gudanar da taron sauyin yanayi a birnin Glasgow ya ce, fitar da iska mai gurbata muhalli a bana za ta kai irin matakin da aka gani a shekara ta 2019, sabanin bara, lokacin da aka samu sassauci saboda takaita hada-hada a sanadiyar cutar Korona.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa, rage fitar da hayaki mai lalata muhalli zuwa kashi 1.5 a ma’aunin Celcius kamar yadda aka cimma a yarjejeniyar birnin Paris, zai takaita yawan mace-mace da barna a yanzu.
Amma a cewar Majalisar Dinkin Duniyar, sai an rage fitar da irin wanann mugun hayakin da kashi da akalla rabi kafin cimma burin rage mace-macen nan da shekara ta 2030.
Sannan sai an daina ma fitar da hayakin baki daya kafin rage mace-macen nan da shekara ta 2050 kamar yadda masana kimiyar ta Majalisar Dinkin Duniya suka bayyana.
Farfesar Sauyin yanayi a Jami’ar East Anglia ta Birtaniya, Corrine Le Quere ta ce, wannan sabon rahoton gaskiya da gaskiya ne, domin kuwa ya nuna ainihin abin da ke wakana a sassan duniya a daidai lokacin da shugabannin kasashe suka hallara a birnin Glasgow don samar da mafita daga matsalar ta sauyin yanayi.