Tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya faɗa wa sashen Hausa na BBC cewa, sata aka je yi gidansa bayan gwamnatin jihar ta ce ta ƙwato wasu motoci daga gidan nasa da gwamnan ya ƙi mayarwa gidan gwamnati.
A ranar Juma’a ne gwamnatin Zamfara ƙarƙashin jagorancin Dauda Lawal na jam’iyyar PDP ta ce jami’an tsaro sun shiga gidajen Matawallae biyu, a Gusau da kuma Maradun, inda suka ƙwato motoci har 40.
Sai dai Matawalle ya ce “sakarci ne” da “talauci” ya sa aka shiga gidan nasa, yana mai cewa an sace kayayyaki ciki har da hijabin matansa.
“Dukkan ɗakunan matana babu wanda ba a shiga ba, har da hijabi na mata aka kwashe. Hatta irin murhun nan na garwashi, duka an saka cikin mota an tafi da su,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin motocin da aka kwashe ya saye su ne daga Amurka tun kafin ya zama gwamna saboda da ma sana’arsa ce sayar da motoci.