Mataimakin gwamnan jihar Sokoto ya karyata labarin da ke cewa ya fita daga jam’iyyar PDP mai mulki a jihar.
A cewar hadiminsa, bai ma san da wasikar da ke yawo ba, inda yace yana nan daram a jam’iyyar ta PDP.
An yada wata wasika a ranar Alhamis da ke nuna yadda mataimakin gwamnan ya fice daga PDP tare da bayyana dalilai.
Manir Muhammad Dan Iya, ya musanta yin murabus daga jam’iyyar PDP mai mulkin jihar.
Aminu Abubakar, daraktan yada labarai na mataimakin gwamnan ne ya fada wa jaridar TheCable ta wayar salula a ranar Alhamis 9 ga watan Faburairu, inda yace mai gidan nasa har yanzy mamba ne na PDP.
A wata wasikar da ta yadu a kafar sada zumunta a ranar Alhamis, an ga rubutun da ke cewa mataimakin gwamnan ya yi murabus daga PDP, ya tura wasikar ga shugaban jam’iyyar PDP na yankinsu.
Bai san da wasikar da ke ta yawo ba Abubakar ya kuma bayyana cewa, mataimakin gwamnan bai ma san da wasikar ba.
Ya ce: “Yanzu na yi magana da mai gida na. “Ba gaskiya bane. Wasikar ba daga wurinsa ta fito ba.
Bai sanya hannu a kanta ba. Har yanzu yana PDP.”
Jita-jitan mataimakin gwamna ya bar PDP A tun farko kun ji cewa, mataimakin gwamnan Sokoto, Manir Dan Iya ya fita daga jam’iyyar PDP mai mulkin jihar.
An ga wata wasika na yawo a kafar sada zumunta, inda aka ce mataimakin gwamnan ne ya rubuta don barin jam’iyyar ta PDP.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da zaben 2023 ke kara gabatowa a Najeriya, jam’iyyun kasar na ci gaba da ganin wani yanayi mai kama da musayar mambobi.
Source:LegitHausa