Mataimakin gwamnan jihar Sokoto, Manir Muhammad Dan Iya, ya yi watsi da maigidansa, Aminu Waziri Tambuwal ana saura yan kwanaki zabe.
Manir Muhammad Dan Iya ya sana da fitarsa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), rahoton DailyTrust.
Dan Iya ya gabatar da takardar murabus dinsa ga shugaban PDP na gundumarsa ta Kware, karamar hukumar Kware ta jihar Sokoto.
A cewar wasikar: “Ina wannan rubutu don sanar da kai janyewata daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) fari daga ranar 8 ga Febriaru, 2023.”
https://twitter.com/DeeOneAyekooto/status/1623614967390806017?ref_src=twsrc%5Etfw%7Ctwcamp%5Etweetembed%7Ctwterm%5E1623614967390806017%7Ctwgr%5E81ca9249754856dda35fabb4db5fd8b73327832f%7Ctwcon%5Es1_c10&ref_url=https%3A%2F%2Fhausa.legit.ng%2Fnews%2F1519062-mataimakin-gwamnan-jihar-sakkwato-ya-yi-watsi-da-tambuwal-ya-fita-daga-pdp%2F
“Na gode bisa damammakin da aka bani, wadanda suka bani damar gudanar da ayyuka da dama karkashin PDP.” Ya watsawa Tambuwal kasa a ido.
Ana ganin cewa wannan babban kalubale ne ga gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, wanda shine Diraktan kamfen shugaban kasan Alhaji Atiku Abubakar.
Duk da bai bayyana manufarsa ba, an kyautata zaton cewa mataimakin na tambuwal zai sanar da komawarsa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
An jima Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasan APC zai dira Sokoto domin gudanar da kamfe.
Zaben sheakarar 2023 dai na gabatowa ne a dai dai lokacin da ‘yan siyasa ke kokarin samarwa da kansu mafaka wacce ta dace dasu a kakar siyasar mai zuwa ta bana.