Dubban masu zanga-zangar yanayi sun jajirce wajen yin tattaki cikin ruwan sama da iska a birnin Glasgow, domin nuna adawa da abin da suka kira gazawar tattaunawar Majalisar Dinkin Duniya kan daukar matakan da suka dace don magance dumamar yanayi.
A Glasgow, masu shirya zanga-zangar da kuma ‘yan sanda sun ce kimanin mutane dubu 50,000 suka yi tattaki a titunan birnin na Scotland.
A makon da ya gabata, wani sabon rahoto da aka wallafa ya bayyana cewa, yawan fitar da iska mai gurbata muhalli zai ta’azzara a cikin wannan shekara ta 2021 zuwa matakin da aka gani gabanin bullar cutar Korona.
Rahoton wanda masu bincike suka wallafa a yayin da kusan kasashen duniya 200 ke gudanar da taron sauyin yanayi a birnin Glasgow ya ce, fitar da iska mai gurbata muhalli a bana, za ta kai irin matakin da aka gani a shekara ta 2019, sabanin bara, lokacin da aka samu sassauci saboda takaita hada-hada a sanadiyar cutar Korona.
A wani labarin na daban kuma Barcelona ta gaza lashe wasan ta na farko bayan korar manaja Ronald Koeman, sakamakon karawar da ta yi da kungiyar Celto Vigo yau asabar wanda aka tashi 3-3.
Fati Vieira ya fara jefawa Barcelona kwallon ta na farko a minti 5 da fara wasa, kafin Busquets ya jefa ta biyu a minti 18, sannan Depay ya jefa ta 3 a minti 34.
Dawowa daga hutun rabin lokaci Iago Aspas ya farkewa Celta Vigo kwallon ta na farko a minti 52, Nolito ya farke na biyu a minti 74, yayin da Aspas ya jefa kwallon sa ta 2 wadda itace ta 3 da Celta Vigo taci a wasan a minti 96.
Wannan ba karamar nasara bace ga Celta wadda ke matsayi na 15 a tebur kafin fara wasan, yayin ta zaam koma baya ga Barcelona wadda a wannan lokaci ke matsayi na 9 a teburin La Liga da maki 17.