Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola a ranar Asabar ya ce masu jagorantar da kuma goyon bayan ta da hankali ga kasar Yarbawa wawaye ne yana cewa “ya kamata su yi la’akari da sakamakon yaki ke haifarwa.”
Aregbesola yayin da yake magana a Otal din Zenabab, Ilesha, Jihar Osun yayin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa ta shekara 64, ya yi gargadin cewa masu son tayar da zaune tsaye dole ne su yi la’akari da mata, yara kanana, tsofaffi da wadanda ke fama da nakasa wadanda galibi abin ya shafa.
Ya ce dole ne Nijeriya ta kara hadewa waje guda idan kasashen Afirka za su sake zama bayi. Ya lura cewa Nijeriya ita ce kasar da za ta ‘yantar da Afirka daga duk wata danniya saboda haka kada ‘yan Nijeriya su yarda da masu ra’ayin ballewa.
Ya kara da cewa “Duk wani abin da ke barazana da haifar da matsala ga Nijeriya na iya haifar da koma-baya ga kasarmu tsawon shekaru 50,”
A wani labarin na daban kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, ya tabbatar da kama wani matashi mai kimanin shekara 15, a jihar Kano bisa zargin ya soka wa matar wansa da ke da juna biyu wuka.
Kamfanin dillacin labaran ya ce, ya samu bayanin ne cikin sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna ya bayar.
DSP Haruna ya ce. da misalin karfe 11 na dare rundunar ta samu rahoton soka wa Malama Habiba Isa mai ciki wata takwas wuka a cikin nata.
Ya ce, nan da nan aka kai ta asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano inda aka kwantar da ita kuma daga baya aka tabbatar da mutuwar dan da ke cikinta.
DSP Haruna ya ci gaba da bayyana cewa matashin ya kai ziyara gidan dan uwansa ne kuma ya bukaci ganin matar, da ya ga ta tsorata tana kokarin kiran mijinta a waya sai ya dauki tabarya ya kabe wayar kuma ya ciro wuka ya soka mata a cikinta da wasu sassan jikinta.