Masana kimiyya fiye da 200 sun bukaci taron kasa da kasa kan sauyin yanayi na COP26 da ya dauki matakin gaggawa don dakatar da dumamar yanayi.
Cikin wata budaddiyar wasika da suka aike, masanan sun yi gargadin cewa, za a shafe daruruwan shekaru ba tare da janyewar wasu daga cikin tasirin sauyin yanayi ba.
Sai dai yayin da tattaunawar kasashe ta masana a taron na COP26 ta shiga kwanaki na karshe, alkawurran da aka yi ya zuwa yanzu na iya haifar da mummunan bala’in karuwar dumamar yanayin zuwa maki 2.7 a ma’aunin Celcius nan da shekara ta 2100, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
A cikin watan Agusta, wani rahoto mai tsoratarwa daga Hukumar Kimiyar Yanayi ta Duniya IPPC, ya yi gargadin cewa matsakaicin zafin duniya zai iya kaiwa matakin maki 1.5 a ma’unin Celcius a shekarar 2030, shekaru goma kafin lokacin da kwararru suka yi hasashen zuwansa.
Hukumar ta IPPC ta kara da cewar, domin dakile kazancewar matsalar dumamar yanayi, dole hukumomi su rage hayaki ko iska mai gubar da suke bulbularwa da akalla kashi 45 cikin 100 nan da shekaru goma.