Ko-odinetan yakin neman zaben Tinubu a Zamfara a zaben da ya gabata, Sanata Kabiru Marafa ya bayyana cewa rashin katsalandan Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu a shari’o’in zaben gwamnoni a kotun koli ya yi matukar ceto dimokuradiyyar kasar nan da kuma farfado da bangaren shari’a.
A ranar Juma’a da ta gabata ce, kotun koli ta raba gardama a zaben gwamnoni guda 8, inda ta tabbatar da nasarar gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, gwamnan Jihar Abiya, Aled Otti da kuma gwamnan Jihar Kuros Riba, Bassey Otu.
Marafa ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, inda ya bayyana cewa Shugaba Tinubu da alkalan kotun koli sun cancanji yabo a wurin ‘yan Nijeriya, saboda sun tabbatar da abun da ‘yan Nijeriya suka zaba.
Ya yaba wa shugaban kasa na kin yin katsalandan, musamman ma a shari’ar gwamnan Jihar Kano wanda ya samu matsin lamba daga magoya bayan jam’iyyarsa.
Marafa ya ce, “Abin farin ciki ne yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai tsoma baki a hukuncin kotun koli ba, haka ya ceci dimokuradiyyar kasar tare da hana sake faruwan abin da ya auko a shekarar 1983.”
Da yake jinjina wa alkalan kotun kolin, Sanata Marafa ya ce sun cika abin da talakawan Nijeriya ke bukata, inda ya ce sun sanya kasar cikin alfahari.
Ya tuno da irin wannan lamari da ya faru zaben 2019, inda a lokacin yake fafatukan neman tikitin takarar gwamnan Zamfara a karkashin jam’iyyar.
Ya ce, “Na yi adawa na nuna rashin amincewa da yadda zaben fid da gwani wajen tsayar da ‘yan takara da Abdulaziz Yari ya samu nasara, inda bangaren shari’a ya tsaya tsayin daka wajen zartar da hukunci da ya bai wa jam’iyyar adawa ta PDP a jihar baki daya.
“Dole ne a bar bangaren shari’a su kasance masu gaskiya da adalci idan ‘yan siyasa suna son dimokuradiyya ta dore a kasar nan.”
Marafa ya bukaci gwamnonin takwas da su kasance masu kankan da kai da adalci wajen tafiyar da mulki a jihohinsu.
Ya taya gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal murna tare da jawo hankalinsa wajen yin aiki domin cika amincewar da al’ummar jihar suka yi masa.
Marafa ya ce, “A saboda haka, ina kira ga gwamnan jiharmu ta Zamfara da ya hada kai da mai girma Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima da hukumomin tsaro domin dawo da zaman lafiya da tsaro da ake bukata a Jihar Zamfara.
Zaman lafiya shi ne abinda jama’armu ke fata ba komai ba.”
Source: LEADERSHIPHAUSA