Manchester City ta lallasa takwarar ta ta Manchester United da ci 2-0 a karawar da suka yi cikin gasar Firimiya a filin wasan Old Trafford, sakamakon da ya dada jefa shakku dangane da makomar manajan kungiyar Ole Gunnar Solksjaer.
‘Dan wasan Manchester United Eric Bailly ya fara jefa kwallon farko a ragar gidan su a minti 7 da fara wasa, kafin daga bisani Bernardo Silva ya jefa kwallo ta biyu a minti 45, abinda ya basu damar samun nasara a karawar.
Mai tsaron gida David De Gea ya taka rawa sosai wajen hana Manchester City jefa kwallye da dama a wasan.
Wannan sakamako na ci gaba da baiwa magoya bayan kungiyar damar bayyana rashin amincewar su da jagorancin Solksjaer ganin yadda kungiyar ta gaza wajen samun karsashin da aka santa da shi, musamman a gasar Firimiya.
Yanzu haka Manchester United na matsayi na 5 a teburin Firimiya da maki 17, yayin da Manchester City ke matsayi na 2 da maki 23.
Sauran sakamakon wasannin da akayi yau a Firimiya sun nuna cewar Chelsea tayi kunnen doki, wato 1-1 da kungiyar Burnley, amma kuma har yanzu itace ke matsayi na farko a tebur da maki 26, sai kuma Crystal Palace da ta doke Wolves da ci 2-0.
Norwich ta doke Brentford da ci 2-1.
Liverpool dai ta kafa tarihin ratatawa Manchester United kwallaye har 5 da nema a gidanta Old Trafford makwanni 2 da suka gabata, rashin nasarar da ta sanya kokwanto ga makomar aikin Solskjear.
Sai dai duk da wannan rashin nasara, United ta iya lallasa Tottenham da kwallaye 3 da nema wanda ya yi awon gaba da aikin Nuna Espirito yayin da kuma ta yi canjaras da Atalanta da kwallaye 2 da 2 karkashin gasar zakarun Turai.
Acewar Solskjear sun dauki babban darasi a shan kayensu hannun Liverpool wanda zai sa su yi taka-tsan-tsan a haduwarsu da Manchester City gobe asabar.
Duk da jerin shan kaye da Manchester United ke yi a wasannin baya-bayan nan matukar ta yi nasara a haduwartata da City kai tsaye kungiyoyin biyu zasu iya dawowa maki dai dai a teburin gasar ta Firimiya.
Karawa tsakanin Manchester City da United dai babban Dabi ne mai cike da tarihi, inda a lokuta da dama suka yi kare jini biri jini ko da ya ke a baya-bayan nan United din ke nasara kan City duk da bajintar Pep Guardiola.
Yanzu haka dai Manchester City ke gaban United a teburi inda ta ke matsayin ta 3 da maki 20 bayan doka wasanni 10 a bangare guda kuma United ke matsayin ta 5 da maki 17.