Rundunar sojin Mali ta sanar da fara gudanar da bincike akan zarge zargen cin zarafin Bil Adama da ake yi wa dakarun kasar yayin yaki da Yan ta’adda.
Masu fafutukar kare hakkin sun dade suna zargin sojojin Mali da aikata laifukan cin zarafin dan adam, da suka hada da kisan gilla, azabtarwa da kuma batar da mutane.
A cikin watan Afrilu, kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta dora alhakin kisan gillar da aka yi wa akalla mutane 34 tare da bacewar wasu 16 akan sojojin Mali yayin gudanar da ayyukansu a tsakiyar kasar a tsakanin Oktoban shekarar 2020 zuwa Maris da ya gabata.
A gefe guda kuma rahoton da aka fitar a shekarar da ta gabata daga tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali, ya zargi sojojin Mali da aiwatar da hukuncin kisa 101 tsakanin watan Janairu zuwa Maris din shekarar ta 2020.
Wani bincike da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar a bara kuwa ya gano shaidun dake nuna cewa jami’an tsaron Mali da masu ikirarin jihadi dukkaninsu sun aikata laifukan yaki.
Mali dai ta dade tana fafutukar kawo karshen kazamin tada kayar bayan da mayaka masu ikirarin jihadi ke yi tun shekarar 2012, kuma tun daga wannan lokaci ya bazu zuwa kasashen Burkina Faso da Nijar da ke makwabtaka da kasar.
A wani labarin na daban majalisar Dinkin Duniya ta ce farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi a duniya a watan Oktoban da ya gabata, mafi tsananin tsadar da aka gani cikin shekaru 10.
A bangaren kayan lambu dai hukumar ta FAO ta ce farashinsu ya karu ne da kashi 9.6 mataki mafi girma da aka taba gani.
Ƙididdigar farashin hatsi kuwa ya karu ne da kashi 3.2 bisa 100, wanda ya haifar da ribar kashi biyar cikin 100 akan alkama, a yayin da adadinta da aka samarwa ya ragu sakamakon matakin rage nomanta da manyan kasashe suka yi.
A dunkule dai farashin kayayyakin abincin da ya karu sau uku cikin watanni ukun da suka gabata, abinda ya sanya hauhawar farashin zama mafi tsanani da aka gani tun bayan watan Yulin shekarar 2011.