Gwamnonin jam’iyyar PDP da ke fushi da jam’iyyar da aka sani da G-5 suna hanyarsu na isa jihar Oyo don kaddamar da takarar tazarcen daya cikinsu, Gwamna Seyi Makinde Majiyoyi sun yi ikirarin cewa.
Gwamna Nyesom Wike da takwarorinsa za su isa Oyo a ranar Alhamis, 5 ga watan Janairu, kuma za su bayyana matsayansu kan dan takarar shugaban kasa da za su goyi baya a 2023.
An kuma tattaro cewa gwamnonin na G-5 za su yi amfani da ralli din don bayyana matsayansu kan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Akwai alamu cewa Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers da takwarorinsa a kungiyar Integrity za su dira Ibadan, babban birnin jihar Oyo, a ranar Alhamis, 5 ga watan Janairu.
Guardian ta tattaro cewa dalilin zuwansu shine kaddamar da yakin neman zabe na ta-zarcen Gwamna Seyi Makinde, Legit.ng ta rahoto.
Kuma, G-5 din za su yi amfani da damar don bayyana matsayan su kan yan takarar shugaban kasa na manyan jam’iyyu gabanin babban zaben 2023.
Don wannan dalilin, kamar akwai zullumi a sansanin jam’iyyar APC, wace Bola Tinubu ke yi wa takarar, da Jam’iyyar Labour da Peter Obi ke yi wa takara, da ake kyautata zaton za su iya zaben daya cikinsu a maimakon Atiku Abubakar wanda ba su ga maciji da Wike da takwarorinsa.
Akwai kuma maganganu daga majiyoyi da ke da kusanci da G-5 din cewa yayin taron, za su yi amfani da damar su jadada dalilan da yasa suke rikici da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarsu.
Daya cikin majiyoyin ya ce: “Za su yi nuni ga inda suka dosa amma watakila ba za su ambaci sunan dan takarar shugaban kasar ba don kada a kama su da laifin cin amanar jam’iyya da kuma kare manufofinsu na siyasa.”
Hakan na zuwa ne yayin da Gwamna Samuel Ortom ya nuna cewa ya karkata ga Peter Obi, duk da cewa sauran takwarorinsa ba su riga sun bayyana wanda za su marawa baya ba.