Shugaba Ra’isi ya jinjna wa ‘yan majalisar kan kokarin da ya ce sun yi wajen ganin sun bin diddigin dukkanin sunayen da ya gabatar domin tabbatar da dacewarsu ko akasin hakan.
Ya ce amincewar da majalisa ta yi da wadannan ministoci ya zo ne bisa gamsuwa da irin kwarewarsu da kuma gogewarsu a bangaren ayyukansu, kuma ya ce yana da tabbaci kan irin kwazon da suke da shi, da kuma kwazon da za su nuna wajen yi wa kasarsu da al’ummarsu aiki.
Sannan ya jaddada cewa, gwamnatin da za a kafa gwamnati ce ta al’ummar kasar Iran baki daya, saboda haka ba za ta yi kasa a gwiwa wajen aiwatar da dukkanin abin da ya rataya a kansu.
Haka nan kuma Ra’isi ya kara nanata aniyarsa ta yin aiki wajen magance matsaloli da dama da kasar take ciki, musamman ma a bangaren tattalin arziki, inda ya ce Iran za ta bayar da muhimmanci wajen gudanar da ayyukan kasuwanci da bunkasa tattalin arziki.