Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya tsawaita aikin Majalisar a kasar Haiti da watanni tara bayan tattaunawar sa’o’i 11, ya haifar da da mai ido tsakanin mayan kasashen yamma da kuma China.
An kada kuri’ar amincewa da tsawaita wa’adin jim sa’o’i kadan kafin wa’adin aikin siyasa ya kare a kasar, inda aka tsawaita shi zuwa 15 ga watan Yulin shekarar 2022.
Yanzu haka kasar Haiti na cikin matsanancin rikicin siyasa, da tattalin arziki da kuma zamantakewa da tsaro.
A wani labarin na daban hukumomin kasar Haiti sun ce adadin mutanen da girgizar kasar da aka samu makon jiya ta kashe ya karu zuwa dubu 2 da 207.
Gwamnatin Haiti ta ce akalla mutane dubu 600 girgizar kasar ta makon jiya ta shafa.
Wata sabuwar barazana kuma da ma’aikatan agaji ke fuskanta a ita ce harin da gungun mutane zauna gari banza ke kai musu, abinda ya haifar da cikas ga aikin raba kayan agaji ga wadanda suka tsira daga iftila’in girgizar kasar.