Ga duk wanda ya tsinci kansa cikin kasar da ake ta fi da mulki karkashin inuwar gwamnatin Dimukradiyya, zai kai ga fahimtar irin aikace-aikace da ke kunshe karkashin ikon Zauren Majalisar Dattawa a Kasa.
Ba kyankyashe dokoki ne ba kadai aikinsu, hatta ma sanya bangaren zartaswa na gwamnati bisa sirdi aikinsu ne, tare da sauran lamura na bibiya, don ganin an samu mirginawar gwamnati bisa nasara a Kasa.
Wannan sansani na majalisar dattawa, waje ne da ke daukar hakikanin fitilar tsarin dimukradiyya a matakin farko. A nan ne ake iya fahimtar karfi, tasiri da tsantsar tsarkin dimukradiyya a Kasa. Shi’isa a duk sa’adda Soja suka yi fashin mulki, majalisar ce ke fara karbar hisabi da hannun hagu, wato, ita ce farkon wadda Sojan za su ce sun ruguje daga wannan rana.
A nan nahiyar Afurka, a duk lokacin da shugabannin Soja ke son yin wani kinburmon da zai nuna sajewarsu da mulkin dimukradiyya, ta nan zauren majalisar ne suke fara coga kartarsu. An samu shugaba Eyadema na Togo, da shugaba Conte na gini, da shugaba Jameh na Gambia da yin irin wannan coge a majalisar. A Najeriya ma marigayi shugaba Abacha, ya tasamma yin irin cogen, na juyewa zuwa ga tsarin dimukradiyya daga soja, sai dai ya kasance mai gajeren kwana ne.
Tun da za mu takaita tsinkayen namu ne ga wannan Jamhuriyar Siyasa ta Hudu (4th Republic) da muke ciki, wadda ta fara daga Shekarar 1999 zuwa yau (2023). Wannan majalisa ta dattijawa, na kunshe ne da tsarin shugabanci iri-iri, faro daga shugabanta na baidaya “Senate President”, mataimakinsa “Deputy Senate President” da sauran manyan kujeru. A nan, za mu so dan yin tsokaci ne game da mataimakan shugabannin majalisar da aka yi, daga Shekarar da wannan jamhuriya ta hudu ta fara mirginawa zuwa yau.
Tsokacin, zai mayar da hankali ne zuwa ga kwazo da nagartar wadannan shugabanni, sai kuma akasin haka. Babu shakka, fitar da amsoshin wadannan tambayoyi, ya fi gaban raraka magana bisa tubalin toka, koko yin molanka sasakai. Lamari ne da ke neman hujjoji na yankan-shakku kuma kwarara.
Irin wancan tankade da rairaya a tsakanin shugabanni na da gayar alfanu iri daban daban, misali;
Shugabannin za su fahimta cewa, al’umar Kasa fa na ankare da su cikin amanonin da suka antaya cikin hannayensu.
Dole ne duk wani shugaba ya rika yin taka-tsantsan, kasantuwar, irin wannan bin-diddigi ga shugabanni, ba zai takaita ba ne ga majalisun Kasa ba kadai. Hatta sauran kujerun majalisun taraiya da na jihohi, akwai yiwuwar nazartarsu nan gaba. Kujerun Kansila, Ciyaman, Gwamba da na shugaban Kasa ma na iya shiga layin titsiyen biro da kididdiga.
Jama’ar Kasa da suka san kansu, na iya marabta da irin wannan bincike ko nazari, wajen sake tunanin irin nau’in managartan mutane da za su ci gaba da rika a matsayin wadanda za su jagorance su, yanzu da nan gaba.
Wadanda sakamakon binciken ya yaba, babu shakka za su kara yin azama wajen kara antayo aiyukan alkhairi ga jama’ar mazabunsu.
Ko shakka babu, wadanda ba su cancanta ba, da marasa kyakkyawan tarihi a jiya, asirinsu na iya tonuwa ne, ta hanyar irin wannan tankade da rairaya, wanda a Turance za a iya kira da “Comparatibe Analysis”!!!.
Daga Shekarar 1999 zuwa yau karkashin wannan Jamhuriyar Siyasa ta hudu, an yi mataimakan shugabannin Majalisar Dattawa “Deputies Senate President” guda biyar (5) ne a wannan Kasa tamu ta Nijeriya Faro daga Sanata Haruna Abubakar, Sanata Ibrahim Mantu, Sanata Ike Ekweremadu, Sanata Oburisi Obie Omo-Agege sannan, da Sanata Barau Jibrin, wanda shi ne ke dare bisa kujerar a yau.
Daga wadancan mataimakan shugabannin majalisar dattawa da aka yi a wannan Kasa cikin jamhuriyar siyasa ta hudu, uku daga cikinsu, Sen. Mantu da Abubakar da Ekweremadu, “ya”yan jam’iyyar PDP ne. Sauran biyun kuwa, Sen. Omo-Agege da Barau Jibrin, sun fito ne daga jam’iyyar APC. Na’am, Sanata Jibrin ya taba yin jam’iyyar PDP, amma ba a matsayin Sanata ba, a matsayin dan majalisar taraiya ne, wato refs “reps”.
Sanata Haruna Abubakar (1)
Sanata Haruna Abubakar ne mataimakin shugaban majalisar dattijai na farko da aka yi cikin wannan jamhuriyar siyasa ta hudu. An haife shi ne a garin Lafiyar jihar Nassarawa, ran 6 ga Watan Yunin Shekarar 1952. Yana da digirinsa na lauya ne da ya yi a jami’ar Ahmadu Bello (ABU) ta Zaria, kuma ya kasance dan siyasa tun a jamhuriyar siyasa ta biyu. Ya samu zama mataimakin shugaban na majalisar dattijai ne a Shekarar 1999.
Sanata Abubakar, ya shiga majalisar ta dattijai a Watan Yunin Shekarar 1999 a matsayin zaba6be, daga mazabarsa ta Nassarawa ta Kudu. Ya sami shiga cikin kwamitittika iri-iri a majalisar, irin kwamitin harkokin shari’a, kwamitin man fetur, kwamitin tattalin arzikin Kasa, kwamitin lamuran basukan gida da waje da sauransu.
Sanata Abubakar, shi ne mataimakin shugaban majalisar dattijai ma fi gajeren zango da aka yi cikin wannan jamhuriyar siyasa ta hudu. A dai cikin Shekarar ta 1999 ne ya yi murabus daga kujerar ta mataimaki, sakamakon tilasa shugaban majalisar dattijai na lokacin, Sen. Eban Enwerem, da aka yi, na dole sai ya yi murabus.
Sanata Ibrahim Mantu (2)
An haifi Sanata Mantu ne a garin Jos din jihar Plateau, ran 16 ga Watan Fabarairun Shekarar 1947 (February 16, 1947). Bayan murabus da Sanata Abubakar ya yi, Mantu ya dare bisa kujerar ta mataimakin shugaban majalisar ta dattijai ne har zuwa Shekarar 2007. Ya yi aiki da shugabannin majalisar har guda uku, Sen. Anyim Pius Anyim, Sen. Adolphus Wabara da Sen. Ken Nnamani.
Sanata Mantu na wakiltar jama’ar mazabar Jos ta tsakiya ne. Sanatan, na da digirinsa ne a fagen sha’anin siyasa, “political science” da ya yi a can jami’ar Washington International Unibersity. Sai dai tun a Shekarar 1978 ne ya shiga siyasar jam’iyya a aikace, ya yi jam’iyyar NPN da farko, daga baya ma ya yi jam’iyyun NRC da UNCP.
Kafin zaman mantu mataimaki a majalisar, ya rike shugaban kwamitin yada labarai na majalisa. Bayan ya zama mataimakin shugaban majalisa kuma, ya zama shugaban kwamitin da zai jagoranci zaurukan majalisun dattijai da na wakilai, don yin kwaskwarima ga Kundin Tsarin Mulki na Kasa, tun daga Shekarar 2001 har zuwa 2007. Ba ya ga wadannan kwamitoci, ya ma shiga wasu kwamitocin da ba a kawo su a nan ba.
Sanata Ike Ikweremadu (3)
Sanata Ekweremadu ne ya karbi kujerar mataimakin shugaban majalisar ta dattawa daga Sanata Mantu, daga Shekarar 2007 har zuwa Shekarar 2019, sannan aka karbe daga hannunsa. An haifi Ekweremadu ne ran 12 ga Watan Mayun Shekarar 1962. Ya samo asali ne daga jihar Enugu. Sannan, yana wakiltar al’umar mazabar Enugu ta yamma ne.
Tun daga digirin farko har zuwa na uku, PhD, Mantu ya yi su ne a fagen shari’a, “law”.
Sanata Obie Omo-Agege (4)
Omo-Agege ne ya sami nasarar kwace waccan kujera ta mataimakin shugaban majalisar dattawa daga hannun Sanata Ekweremadu, bayan gabatar da zabe a majalisa.
Shi ma Omo-Agege da aka haifa ran 3 ga Watan Augustan Shekarar 1963, karatun lauyanci ne ya karanta kamar wasu daga takwarorinsa. Kuma yana wakiltar jama’ar mazabar Delta ta tsakiya ne, daga Shekarar 2015 zuwa 2023.
Sanata Barau Jibrin (5)
Sanata Barau Jibrin ne mutum na biyar da ke rike da wannan kujera ta mataimaki a yanzu haka. Kamar yadda Omo-Agege ya zamto wani mutum na farko daga Delta da ya sami damar darewa bisa wannan kujera ta mataimakin shugaban majalisar dattijai ta Kasa, haka shi ma Sanata Jibrin, shi ne mutum na farko daga jihar Kano bakidaya da ya sami damar dare wannan kujera cikin nasara.
An haifi Barau ne ran 1 ga Watan Janairun Shekarar 1959, haifaffen birnin Kabo ne, Kano. Ya karbi kujerar Sanata ne a matsayin mai wakiltar al’umar Kano ta arewa, daga hannun Sanata Bello Hayatu Gwarzo, na jam’iyyar PDP. Gabanin zama Sanata, Barau Jibrin, ya yi dan majalisar taraiya mai wakiltar jama’ar karamar hukumar Tarauni, Kano, daga Shekarar 1999 zuwa 2003.
A wannan zubin majalisa ta goma (10) Sanata Barau Jibrin ya yi habzi da wannan kujera ta mataimakin shugaban majalisar dattijai ta Kasa a taraiyar Nijeriya Bayan samun kuru’u mafiya rinjaye da shi da shugaban majalisar dattijan na yanzu, Sanata Godswill Akpabio, inda suka rantama dan takarar tsagin su Sanata Kawu Sumaila da kasa.
Ba ya ga digirin farko a kididdiga da lissafi “Accounting”, Sanata Barau ya yi wasu digirori na biyu biyu har sau uku “master’s degree” a wasu fagage iri iri da suka kunshi gudanarwa da tafikad da aiyukan ofis da harkokin kasuwanci. Bugu da kari, yana ma da wasu takardun shaidar karatun da ba a gabatar da su a nan ba. Ya yi karance karancen nasa ne a nan gida Najeriya da ma Kasashen Waje, cikinsu har da Amurka.
Sanata Barau, ya rike kwamitoci iri iri a majalisar, a wasu kwamitocin, shi ne shugaba, a wasu kuma yana daga kunshin kwamitin ne, faro tun daga lokacin da yake dan majalisar wakilai zuwa lokacin da ya shige majalisar dattijai. Ya jagoranci kwamitin manyan makarantu na gwamnati da na hukumar Tetfund. Haka ya jagoranci kwamitin kasafin kudi da kwamitin wutar lantarki da sauransu.
Sanyawa A Sikeli Tare Da Kididdigewa
Abu na gaba da wannan rubutu zai mayar da hankali a kai shi ne, cikin wadannan Sanatoci biyar (5), wadanda suka jagoranci kujerar mataimakin majalisar dattijai, yaya nauyinsu, jajurcewarsu da kuma ingancinsu yake a siyasance, a ciki da wajen majalisar?
Source: LEADERSHIPHAUSA