Maharan da suka yi garkuwa da yan uwan malamin jami’ar nan na jihar Zamfara sun nemi a biya su naira miliyan 70 a matsayin kudin fansa Bukatar tasu na zuwa ne kasa da kwana guda bayan da suka kwashi mutum 5 daga gidan malamin, Abdulrahaman Adamu a yankin Damba a ranar Laraba Mista Abdulrahaman ya tabbatar da cewar maharan sun kira sun kuma nemi a basu kudin, sai dai ya ce a taya su da addu’a.
Yan bindigar da suka yi garkuwa da yan uwan wani malamin jami’a a jihar Zamfara sun nemi a biya naira miliyan 70 a matsayin kudin fansar sakinsu.
Wannan na zuwa ne kasa da kwana daya bayan maharan da suka farmaki gidan Abdulrahaman Adamu da ke Damba Quaters, a wajen Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, sannan suka sace mutum biyar.
Yan awanni bayan faruwar lamarin, wata majiya ta iyalin wacce ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da cewar masu garkuwa da maharan sun kira su, Channels TV ta rahoto.
A cewarsa, sun bukaci a biya naira miliyan 70 a matsayin kudin fansa kafin su saki yan uwan nasu.
Hakazalika Mista Abdulrahman ya shaidawa TVC News cewa maharan sun kira suna neman a basu naira miliyan 70 kafin su sako yan uwan nasa.
Ya yi kira da a kara taya shi da addu’o’i domin yan uwansa su dawo gida lafiya. Majiyoyi sun shaidawa Channels TV cewa maharan sun aiwatar da harin ne a safiyar ranar, inda aka kuma sace wani da ya kasance jami’in jami’ar.
Wadanda aka sace sun hada da kanin shugaban ASUU din, yar kaninsa, dan kaninsa da kannen matansa biyu.