Makonnin takwas da suka gabata aka yi garkuwa da Mahaifin kakakin Majalisar, Muazu Abubakar tare da mai dakinsa dauke da jariri mai makonni uku, da Malam Magarya da kuma wasu mutum biyu.
Kogi;
A wani labarin kuma, tsohon shugaban Kwalejin Ilimi ta Jihar Kogi da ke Kabba, Julius Oshadumo, wanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi makwanni biyu da suka gabata, ya mutu a rikicin da ya barke tsakanin masu garkuwa da shi da jami’an tsaro, yayin da ake kokarin aikin ceton sa.
An yi garkuwa da jimi’in ne makonni biyu da suka gabata lokacin da wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka kai hari kan cocin ECWA da ke yankin Okedayo a Kabba ta Jihar Kogi, inda aka kashe mutum daya sannan aka raunata wasu masu ibada.
A wani labarin na daban dai Najeriya, Mazauna karamar hukumar Kankara na jihar Katsina sun shiga rudani sakamakon kwararar ‘yan bindiga da ake zargi masu tserewa ne daga Zamfara.
Wani mazaunin kauyen Pawwa, ya shaidawa jaridar cewa ‘yan bindigar sun kafa shinge inda suke binciker mutanen da ke wucewa tsakanin titin Kankara zuwa Zango.
A cewar mutan yankin “Babban bukatar ‘yan bindigar yanzu shi ne samun abinci da man fetur, suna dauke da jarkoki, inda suke karbar wani adadi na mai daga masu ababen-hawa da kwace duk wani abinci da suka gani.”