Gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu ya jinjinawa Tinubu akan tsarin sa da manufofin sa na ci gaban Najeriya da kuma bukatar samar masa da goyan bayan da ake bukata domin samun nasarar bukatar sa ta jagorancin Najeriya.
Sanwo-Olu yace masu goyan bayan wannan shiri sun yi amanna da jagorancin Tinubu da saukin kan sa da kuma aniyar sa ta samar da ci gaban Najeriya a matakai daban daban.
Taron ya samu halartar mutane da dama dake goyan bayan manufofin jagorar APC Bola Ahmed Tinubu, wanda ya taka rawa sosai wajen kafa gwamnatin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke jagoranci.
Rahotanni sun ce magoya bayan Tinubu na bayyana shakku dangane da shirin jam’iyyar APC na bashi takarar zabe mai zuwa duk da alkawarin da akayi masa lokacin da ya marawa shugaban kasa Buhari baya a shekarar 2015 da 2019.
Sai dai wasu ‘yayan Jam’iyyar APC suna cewar babu wata yarjejeniyar da akayi na cewar bayan kare wa’adin mulkin Buhari za’a baiwa Tinubu damar tsayawa takara a shekarar 2023.
Tuni wannan takun sakar ya fara raba kawunan ‘yayan Jam’iyyar, abinda ya sa wasu magoya bayan Tinubu ke zargin cewar an kama hanyar cin amanar su.
Wasu daga cikin gwamnonin APC dake da karfin fada a ji sun bayyana matsayin su na ganin mulkin Najeriyar ya koma kudancin kasar, amma kuma matsayin da gwamnonin kudancin kasar 17 suka dauka na neman tilasta karba karbar na neman barin baya da kura, ganin yadda suma gwamnonin arewa 19 suka ce ba’a siyasa da tirsasawa, saboda haka babu batun karba karba a kundin tsarin mulki.