Fitacciyar ‘yar siyasar mai shekaru 62, da ta sake lashe zabe karo na 2 a matsayin magajin garin Paris a shekarar da ta gabata, ta samu yabo daga bangarori da dama kan tsarin gudanar da ayyukan ta a babban birnin Faransa.
A lokacin shugabancin Anne Hidalgo al’amura daban daban sun dauki hankalin duniya a birnin Paris, da suka hada da jerin hare-haren ta’addanci a shekarar 2015, zanga-zangar adawa da gwamnati ta Yellow Vest, mummunar gobarar da ta kone dadaddiyar mujami’ar Notre-Dame, barkewar annobar Korona, sai kuma nasarar da birnin na Paris ya samu dangane da karbar bakuncin wasannin gasar Olympics a 2024.
A wani labarin na daban tsohon Firaministan Faransa Edouard Philippe na shirin tsayawa takara a zaben shugaban kasar mai zuwa, abin da ake kallo a matsayin wata barazana ga shugaba Eammanuel Macron a siyasance.
Bayan ajiye mukamin nasa, Philippe ya kuma fice daga jam’iyya mai mulkin kasar ta Macron tare da komawa jam’iyyar hamayya wadda karkashinta ne zai tsaya takarar don kalubalantar tsohon ubangidansa.
Masharhanta kan siyasa a kasar na ganin cewa, Philippe ka iya zama babbar barazana ga Macron a yayin zaben, kasancewar Macron din ya amince masa matuka lokacin da yake Firaministan.
A zamanin da yake rike da mukamin siyasa ,Philippe shi ne shugaban Hukumar Kula da ‘Yan Fansho ta kasar, kuma ya taka rawar gani matuka.