Akalla mutane hudu aka tabbatar da mutuwar su yayin da wasu biyar suka samu raunuka bayan da wani bene mai hawa uku ya yuguje a birnin Lagos dake Kudanci Najeriya.
Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Lagas, Ibrahim Farinloye ne ya bayyana hakan a safiyar ranar Lahadi.
Rahotanni na cewa benin mai hawa uku da ba’a karasa ginawa ba ya rikoto ne yayin da ake ruwan sama kamar da bakin kwarya a yankin a ranar Asabar.
Jami’an yace asalin ginin bungalow ne, amma ake kokarin mai da shi hawa uku.
Jihar Legas dai ta yi kaurin suna wajen rugujewar gine-gine a ‘yan kwanakin nan, lamarin da ya janyo hasarar rayuka da jikkatar mutane da dama.
Na baya-bayan nan shine wanda wani bene mai hawa uku ya ruguje a Ebute Metta,ranar 1 ga watan Mayun, inda mutane akalla 10 suka mutu.
A wank labarin na daban kuma ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da shirin kafa manya-manyan sansanonin sojinta a yankin yammacin kasar don martini ga NATO kan dauki dai-dai da ta ke yiwa kasashen gabashin Turai, matakin da ke zuwa dai dai lokacin da wasu Sojin Ukraine kusan dubu 2 suka mika wuya ga Moscow.
Ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu ya ce kafa sabbin sansanonin Soji wajibi ne a garesu don dakile barazanar da kasar ke fuskanta daga kungiyar da ta kira babbar makiyiyarta wato NATO.
A wata sanarwar kai tsaye da ministan tsaron Sergei Shoigu ya yi ta gidan talabijin, ya bayyana cewa zuwa nan da karshen shekara za su samar da sansanonin Soji akalla 12 a yammacin kasar, wadanda za a wadata da manyan makaman kare kai.
Bayan matakin shugaba Vladimir Putin na aikewa da dakaru Ukraine a ranar 24 ga watan fabarairun da ya gabata lamarin da ya yamutsa zaman lafiyar duniya, matakin ya sanya kasashen Finland da Sweden da suka shafe shekaru a matsayin ‘yan ba ruwanmu neman izinin shiga NATO.
Dai dai lokacin da yakin na Rasha da Ukraine ke ci gaba da tsananta, zuwa yau juma’a akalla Sojin Ukraine 1908 suka mika wuya bayan da ma’aikatar tsaron kasar ta umarce su da su ajje makamansu don neman maslaha da Rasha.
Wasu bayanai sun ce gwamnatin Ukraine na son musayar dubunnan sojojin da Rasha ta akme mata da fursunonin Moscow da yanzu haka ke hannunta.