Wani rahoto dake yawo ya ja hankalin mutane inda ake cewa Kwankwaso na shirin janye wa ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar.
Sai dai jam’iyyar NNPP ta bakin shugabanta na ƙasa, Rufai Alkali, da kakakinta, Major Agbo, sun karyata rahoton.
A cewar NNPP ganin yadda Kwankwaso ke ƙara karbuwa ne ya haddasa tsoro a zukatan wasu.
New Nigeria Peoples Party (NNPP) tace ɗan takararta na shugaban kasa a zabe mai zuwa, Rabiu Kwankwaso, ba zai janye wa takwaransa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ba.
Kakakin jam’iyyar NNPP na ƙasa, Major Agbo, shi ne ya bayyana haka yayin zantawa da jaridar Punch, ya musanta jita-jitar cewa manyan arewa sun matsa wa Kwankwaso ya janye wa Atiku.
Da yake martani kan raɗe-raɗin dake yawo, Agbo yace, “Ta ya wani zai shaƙi iska yace Kwankwaso ya janyewa Atiku? Ba zai yuwu ba, Atiku ne ya kamata ya janye.”
A cewarsa, Kwankwaso ya shiga tseren takara ne domin yana a karfin samun nasara, ya kuma jaddada cewa ɗan takarar NNPP ne zai zama shugaban Najeriya na gaba.
Sai dai mai magana da yawun jam’iyyar NNPP bai kore batun cewa suna tattaunawar ƙawance da wasu ba, wanda acewarsa zai yuwu ne kan tsari da aka amince da shi.
Shin har yanzu Kwankwaso na tattaunawar sulhu da Peter Obi?
Yayin da aka nemi ya yi ƙarin haske kan matakin da ake a tattaunawar haɗa kai tsakanin NNPP da Labour Party, Agbo ya yi watsi da rahoton ana ci gaba da tattaunawar.
“Ku je ku tambayi Okupe, shi ne ya fara ruguza tattaunawar haɗin guiwa ta farko saboda ya zo da wata manufa cewa Obi ne zai zama ɗan takarar shugaban kasa.
Ta ya Obi zai hau saman Kwankwaso?”
Sun fara tsorata da Kwankwaso – Alƙali Haka nana shugaban NNPP na ƙasa, Rufai Alkali, ya yi magana makamanciyar ta Mista Agbo, inda ya ayyana rahoton da tsagwaron ƙarya.
Yace, “Ƙarya ne, bamu yi mamaki ba, da farko ance ɗan takararmu zai janyewa Tinubu, muka ƙaryata sai kuma aka ƙara cewa NNPP ta miƙa wuya ga LP da Obi.
Da muka hito muka yi bayani sai suka yi shiru.”
“Yanzu kuma bayan duk manaƙisar da aka shirya a taron da manyan arewa suka shirya muka ƙi zuwa, an zo da wata sabuwa wai ɗan takararmu na shan matsin lamba ya janye, to ya janye wa wane?”
“Saboda yanzu ya zama tauraro, sun tsorata shi ne aka koma yaɗa farfaganda duk masu hannu a wannan lamarin ya kamata su saduda hakanan.”
A wani labarin kuma Jam’iyyar NNPP ta Kwankwaso ta samu gagarumin goyon baya a jihar Gombe dake arewacin Najeriya
Rahoto ya nuna cewa Bola Tinubu da Atiku Abubakar sun yi rashin magoya baya yayain da mambobin PDP da APC suka sauya sheƙa zuwa NNPP a Gombe.
Masu sauya sheƙar sun samu kyakkyawar tarba daga ɗan takarar gwamnan jihar na NNPP kuma ana ganin wannan karin ƙarfi ne ga tsohon gwamnan Kano.
Source:LEGITHAUSA