Tsohon Gwamnan Jihar kano dake Najeriya Rabiu Musa Kwankwaso ya kawo karshen zamansa a cikin Jam’iyyar PDP sakamakon sanarwar da yayi na ficewa daga cikin ta.
Tsohon gwamnan ya ce sakamakon wasu dalilai na rashin fahimtar juna, ya yanke hukuncin ficewa daga jam’iyyar daga yau Talata, 29 ga watan Maris na shekarar 2022.
Kafin dai wannan lokaci an dade ana rade radin cewar Kwankwaso zai sauya sheka zuwa Jam’iyyar NNPP domin tsayawa takarar zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa.
Tuni wasu daga cikin magoya bayan sa suka fice daga PDP domin komawa sabuwar Jam’iyyar a Jihar Kano da kuma wasu jihohi dake cikin kasar.
A wani labarin na daban Jamhuriyar Demokuradiyar Congo ta zama cikakkiyar mamba a Kungiyar Kasashen Gabashin Afrika ta EAC wadda ke gudanar da hada-hadar kasuwancin bai-daya a tsakanin mambobinta da kuma bai wa al’ummar yankin damar zirga-zirgarsu kai tsaye cikin kasashen yankin.
Shugaban Kungiyar ta EAC kuma shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta, shi ne ya sanar da karbar Jamhuriyar Demokuradiyar Congo a matsayin sabuwar mamba, matakin da ya bayyana da wani sabon tarihi.
Yanzu haka wannan kungiya ta kara samun fadin kasa wanda ya taso daga Tekun India har zuwa can Tekun Atlantic, abin da ya sa kasashen kungiyar suka kara samun damar damawa da su a fagen goyayyar kasuwanci a nahiyar Afrika.
Tun dai shekara ta 2000 ne dai, aka kafa wannan kungiyar, inda ta yi aiki tukuru wajen karfafa hada-hadar kasuwanci ta hanyar cire kudaden fito a tsakanin mambobinta, yayin da a shekara ta 2010, ta assasa kasuwancin bai-daya.
Yanzu haka Jamhuriyar Demokuradiyar Congo mai yawan al’umma miliyan 90 wadda kuma ke da arzikin karkashin kasa, za ta fadada kasuwancin kungiyar zuwa kusan na mutane miliyan 300.