Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bukaci ‘yan siyasa su gina jama’a maimakon sace dukiyoyinsu.
Kwankwaso ya yi wannan nasihar ne a Minna a ranar Alhamis a lokacin da ya zama shugaba a wajen taron kaddamar da zababben gwamnan jihar Neja, Mohammed Bago.
Tsohon gwamnan ya bukaci zababben gwamnan da ya maida hankali sosai a fannin ilimi da tsaro domin amfanin jihar Neja ko kuma zai yi nadama a nan gaba, ya kara da cewa jarin da ake zubawa a fannin ilimi na iya yiwuwa ba za a ga tasirinshi ba nan take amma a karshe za a ga sakamako mai dimbin yawa.
Ya kara da cewa, Bago ya zama gwamna mai taka rawar gani, dole sai ya kama aiki tukuru bayan an rantsar da shi don cigaban tattalin arziki da jin dadin zamantakewar al’ummar jihar.
Ya bayyana cewa rashin aiki da ilimi ya sa gwamnoni da dama ba su da wani abin a zo a gani a jihohinsu bayan shekaru hudu ko takwas na mulki da suka yi.
A wani labarin na daban sabon shugaban karamar hukumar Karasuwa a jihar Yobe da aka nada kwanan nan, Honorable Lawan Gana Karasuwa ya rasu.
A wata sanarwar manema labarai dauke da sanya hannun darakta Janar kan harkokin yada labarai na ofishin gwamnan Jihar, Mamman Mohammed ya ce, Gana ya rasu ne a asibitin Gwamnatin tarayya (FMC) Nguru bayan gajeruwar rashin lafiyar da ta riske shi.
LEADERSHIP ta labarto cewa marigayin ya taba zama Shugaban riko na karamar hukumar Karasuwa na waya shida kafin gwamnan Jihar Mai Mala Buni ya sauke su.
Yana daga cikin shugabannin riko 17 da gwamnan ya nada da za a rantsar da su a gobe Juma’a.
Wani abokinsa, Hon. Ado Adamu Bomboy, ya misalta marigayin a matsayin mutum mai kirki, kamala da dattako.