Tsohon Gwamnan jihar Kano Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso ya fito da kansa yayi watsi da maganar ya yiwa wani alkawarin janyewa daga takara.
Kwankwaso ya zargi yan jarida da rashin adalci wajen yada rahotannin su kuma ya basu shawara.
Hanarabul Jibrin yace babu dan siyasan da ya kai Kwankwaso shahara a duk fadin Arewacin Najeriya.
Dr Musa Rabiu dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), a zaben 2023 ya yi watsi rahotannin dake yawo a kafafen yada labarai.
Dan takarar shugaban kasan na jawabin da ya fitar ranar Asabar, 27 ga Agusta a shafinsa na Tuwita ya bayyana cewa ko kadan babu wata yarjejeniya da yayi da wani na janyewa daga takarar kujerar shugaban kasa.
Tsohon Gwamnan Kanon hakazalika ya yi kira ga yan jarida su rika adalci da gaskiya wajen yada rahotanninsu.
A cewar Kwankwaso: “Ban shiga wata yarjejeniyar da zata sa in janyewa wani a takarar nan ba.
Saboda haka ina kira ga al’umma suyi watsi da wannan labari.”
“Hakazalika ina kira ga yan jarida su rike mutunta aikinsu ta hanyar yin adalci wajen bada rahotanninsu.”
Ai Tuni Kwankwaso Ya Gaje Farin Jinin Buhari a Arewa:
AbdulMumini Jibrin Tsohon dan majalisar wakilai kuma Kakakin yakin neman zaben jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), AbdulMumini Jibrin ya ce Kwankwaso ya gaje farin jinin Shugaba Buhari a Arewa.
Jibrin ya bayyana hakan ne a hirar da yayi a tashar Channels, TheCable ta gano.
Jibrin ya bayyana hakan yayin mayar da martani kan maganar cewa Kwankwasoo na shawarar janyewa Tinubu na APC.
Ya ce babu dan takara da ya kai Kwankwaso kuri’u a Arewacin Najeriya.
Source: LEGITHAUSA