Kwamitin wucin gadi na Majalisar Dokokin Jihar Kaduna da ke binciken yadda aka gudanar da harkokin kudi a karkashin gwamnatin Gwamna Nasir el-Rufai, ya gayyaci tsoffin kwamishinoni da manyan sakatarori da wasu shugabannin kananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki a gwamnatin da ta gabata.
Idan dai za a iya tunawa, majalisar ta kafa kwamitin ne domin ya binciki harkallar kudaden jihar, lamuni, kwangila da sauransu daga ranar 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 29 ga watan Mayun 2023 a lokacin da El-Rufai yake gwamnan jihar.
Shugaban kwamitin Hon. Henry Magaji Danjuma, wanda ya zanta da manema labarai bayan wata tattaunawa ta sirri da tsoffin hadiman El-Rufai a daren ranar Litinin, ya ce: “Mun ga ya zama dole mu tattauna da su domin cimma nasara da kuma bayar da sahihin rahoton kwamitinmu.”
Hon. Danjuma, wanda shi ne mataimakin kakakin majalisar, ya ce, an bai wa duk wadanda aka gayyata dama ta musamman.
Tun da farko dai, kwamitin ya fara tattaunawa da tsoffin shugabannin majalisun jihar na 8 da 9, Hon. Aminu Shagali da Hon. Yusuf Zailani a makon da ya gabata.
A wani labarin na daban babban bankin Nijeriya (CBN), ya bai wa bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi umarnin fara cire harajin kashi 0.5 don tsaron yanar gizo.
CBN, ya ce harajin za a yi amfani da shi wajen yaki da masu datsar bayanan mutane ta yanar gizo kan harkar sha’anin banki.
Umarnin wanda ya bayyana a wata takardar da ke dauke da sa hannun daraktan sashen kula da tsarin biyan kudi, Chibuzo Efobi, da Haruna Mustafa, daraktan sashen tsare-tsare na kudi na CBN, ya bayyana cewa za ake cire sabon harajin ne a duk lokacin da mutane ya tura kudi.
Harajin zai fara aiki nan da makonni biyu daga ranar Litinin, kamar yadda CBN ya bayyana.
DUBA BAN: Babbar Kotu Ta Dakatar Da Kama Tsohon Gwamna Ganduje
Amma babban bankin ya ce akwai akalla hada-hadar kudi 16 da sabon harajin bai shafa ba: