Kungiyar kwadago da Kungiyar ‘Yan kasuwa su na tare da Jam’iyyar Labor Party a zabe mai zuwa.
Shugabannin NLC da na TUC sun tabbatar da haka a wajen taron tunawa da Marigayi Pascal Bafyau Ayuba Wabba ya ce wannan ne karon farko da ma’aikata za su goyi bayan ‘dan takaran LP a zabe.
Kungiyar kwadago ta Najeriya watau NLC, da takwararta TUC ta ‘yan kasuwa, za su marawa Peter Obi baya ne a zaben shugaban kasa na 2023.
Vanguard ta ce wadannan kungiyoyi sun sha alwashin nan a ranar Talata, 28 ga watan Yuni 2022. Shugaban NLC na kasa, Ayuba Wabba da shugaban TUC, Quadri Olaleye sun yi alkawari sai inda karfinsu ya kare wajen ganin Peter Obi ya yi nasara a zaben.
Wabba da Olaleye sun sha wannan alwashin a hedikwatar kwadago na Pascal Bafyau Labour da kuma sakatariyar TUC da suke babban birnin tarayya Abuja.
The Nation ta ce shugabannin kwadago sun yi wa ma’aikata jawabi a jiya a wajen wata lacca ta musamman da aka yi domin a tuna da Marigayi Pascal Bafyau.
A jawabinsa, Wabba ya bayyana Peter Obi a matsayin lafiyayyen ‘dan takarar shugaban kasa.
Twitter Shugaban kungiyar ta NLC ya ce Obi ne ‘dan takarar jam’iyyar LP na farko da ‘yan kwadago za su marawa baya a zaben shugaban kasa, ya ce za su tsaya masa.
An ji Wabba yana cewa ma’aikata sun fahimci yajin-aiki ba zai iya kawo karshen rashin adalcin da ake yi masu ba, a dalilin haka suka ga bukatar shiga siyasa.
Mun yi mubaya’a inji TUC Da yake na shi jawabin, Olaleye ya ce sun karbi Obi a matsayin ‘dan takarar da za su yi aiki da shi, kuma duk za su kada masa kuri’arsu a zaben shugaban kasa.