Jam’iyyar NNPP ta ce kwace mata zaben da ta ci a Jihar Kano, zai iya janyo tashin hankalin da zai yadu zuwa sauran kasahen Afirka.
Wata sanarwa da mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Abba Kawu Ali, ya fitar, kuma babban jami’i mai binciken kudi na jam’iyyar, Ladipo Johnson ya karanta a gaban ofisoshin jakadancin Kasashen Yamma a ranar Laraba, NNPP ta yi ikirarin cewa akwai alamun da ke nuna cewa ana yunkurin yi wa zaben Kano murdiya.
Mambobin jam’iyyar suna ci gaba da zanga-zanga a Kano tun bayan hukuncin kotun daukaka kara da ya sake tabbatar da soke nasarar gwamna Abba Kabir Yusuf.
A ranar Laraba kuma, magoya bayan jam’iyyar sun yi zanga-zanga zuwa ofisoshin Tarayyar Turai da ofishin jakadancin Amurka da na Birtaniya da kuma Hukumar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) don neman a yi musu adalci,
Sun dnuna bacin ransu kan hukuncin zaben gwamnan Kano da kotun daukaka kara ta yanke a kan zaben gwamnan Jihar Kano.
Ladipo Johnson ya ce tuni hankali ya tashi a Kano bayan ganin yadda mutane suka nuna rashin jin dadin magudin zaben da aka musu a 2019.
Ya ce jam’iyyar ba za ta yi wasa da kundin takardar hukuncin kotun daukaka kara wanda ya ayyana Gwamna Abba a matsayin wanda ya ci zabe.
“Yayin da NNPP ta garzaya zuwa Kotun Koli don bin kadinsu, mun damu da batun zama lafiya, musamman a Jihar Kano da kuma Arewacin Nijeriya. Don haka, muna son Kotun Koli da ta yi adalci wajen dawowa da al’ummar Kano da gwamna Abba Kabir Yusuf hakkinsu.
“Yayin da muka tunkari kotun karshe, hankali ya tashi a Kano,” in ji NNPP.
NNPP ta ce tana son fada wa shugabannin duniya cewa abin da ake shirin yi ba abu ne mai kyau ga Nijeriya kadai ba, har ma da Afirka da kuma duniya baki daya.
Idan ba a manta dai kotun daukaka kara ta soke nasarar gwamna Abba, inda ta ce ba dan jam’iyyar NNPP ba ne a Jihar Kano.
Source: LEADERSHIPHAUSA