Aiwatar da wannan doka za ta bukaci manyan bankunan kasashen Turai da su rika adana tarin kudade a asusunsu.
Kazalika sabbin ka’idojin hada-hadar kudaden, za su tilasta wa bankunan fitar da bayanai game da hadarin da suke fuskanta kan sauyin yanayi ta hanyar samar da kudaden gudanar da ayyukan da suka shafi gurbata muhalli.
Kodayake ana sa ran dokar ta kan-kama sosai nan da ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2025 kamar yadda mataimakin shugaban Kungiyar Tarayyar Turai, Valdis Dombrovskis ya shaida wa manema labarai.
A bangare guda, manyan bankunan Turai sun yi ta neman kamun-kafa da hukumomin nahiyar domin ganin an sassauta tsauraran ka’idojin dokar, suna masu cewa, rashin daga-musu-kafa ka iya janyo musu asarar wasu kudaden riba.
A wani labarin na daban jami’an tsaro sun chafke akalla mutane 150 da ake zargi da hannu wajen aikata laifukan damfarar mutane ta intenet, a fadin duniya, a cewar rundunar ‘yan sandan tarayyar Turai.
Ana zargin mutanen da aka kama da hannu wajen kirkirar haramtattun shafukan Intenet domin damfarar mutanen ta hanyar sayar musu da kayayyaki marasa inganci, ko kuma kulla kasuwanci na bogi da sauran laifuka.
Sashen ‘yan sandan turai na Operation DarkHunTOR ne ya kaddamar da aikin kama mutanen, wanda kuma aka kwato miliyoyin euro na tsabar kudi da kuma kudaden Intenet na Bitcoin da bindigogi da kuma muggan kwayoyi.
‘Yan sandan sun ce alamu na nuni da cewa aikata badakala ta kan interenet na sake samun gurin zama a zukatan jama’a musamman matasa ta yadda suke samar da kasuwanni na bogi don karbewa mutane kudade da kadarorinsu.
An dai kama mutanen ne a kasashen Australia, Bulgaria, France, Germany, Italy, Netherlands, Switzerland, Burtaniya da kuma Amurka.
Sojojin sun ce sun kama mutane 65 a Amurka sai guda 47 a Jamus, 24 aka kama a Birtaniya da kuma 4 a Italiya da Netherlands.